Magama Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman | Page 11

u w k u h kec I OKEAGU - @ikechukwuokeagu ya fara sarrafa hotuna tun yana xan makarantar Sakandare. Kayan aikinsa (na wancan lokacin) ita ce kyamarar xaukar fim ta Yashica, sannan ya kasance mai takatsantsan lokacin da yake xaukar hotunan bisa la’akari da irin kuxin da ake kashewa da tsawon lokacin da ake xauka wajen wanke dodon hoto. Wannan yunqurin wuri da ya soma, shi ya haifar masa shiga da qwarewa a hada-hadar xaukar hotuna da shirya fina- finai, har ta kai ya samu halartar mashahuriyar makarantar nan ta horar da masu shirya fina- finai da ke Jos a Jihar Filato. Kuma a halin yanzu yana aiki tuquru kan xaukacin dabarun sarrafa hotuna, inda ya fi bayar da fifikon muhimmanci kan hotunan tafiye-tafiye (yawon buxe ido) da suka danganci ziyarar muhalli mai qayatarwa, inda tsirrai da namun daji ke walwala. A wajen mutusmin da a kodayaushe sha’awarsa ita ce tafiye-tafiye, ya haxu da mutanen da a da bai san su ba, ya gano sababbin wurare, ziyarar wuraren da yake xaukar hotuna ya xamfaru da ita ne kawai. Irin wannan sha’awa da ta xamfaru a rayuwarsa ta yi matuqar taimakawa wajen xauko hoto mai ban sha’awa da qayatarwa, har ta kai ga ya samu daraja ta uku a gasar xaukar hotunan wurare da abubuwa masu qayatarwa ta NairaGEMs. Baya ga cewa, shi ne shugaban xakin sarrafa hotuna na Jabe Studios, wani katafaren wurin haxakar sarrafa sauti da hotuna masu motsi a Abuja, Ikechukwu yana aiki kan wani littafin ko kundin hotunan da bai yi wa laqabi ba, inda yake buqatar ganin ya wallafa hotunan tafiye- tafiye, ta yadda zai zubarar tare da ankarar da duniya, ta hanyar baje-kolin kyawawan wurare da abubuwan da ake iya gani ko samu a xaukacin faxin Najeriya. Da aka tuntuve shi kan yadda aka yi ya yi tasiri a gasar, sai ya ce, “Shiga gasa ta sanya na goge da mu’amala da sababbin mutane (waxanda a da ban san su ba) tare da al’adu da halartar wuraren da ban tava zuwa ba. Na qulla abota da sauran waxanda suka shiga gasar, waxanda muka yi musayar fahimta da dabaru. Basirata ta bunqasa, inda idona ya buxe wajen qulla hulxar dangantaka da mutanen da ke sha’awar irin ayyukan da nake yi, wannan shi ya sake zaburar da ni har na cika da zaquwar son inganta ayyukan da nake qirqira.” Ikechukwu ya samu kyautar kyamarar xaukar hoto samfurin Canon EOS Rebel T7i bisa qimanta darajar hoton da ya shiga gasar da shi, kuma yanzu ita ce makamin aikinsa a tafiye- tafiyen da zai yi wajen xaukar hotuna na tsaye cak da masu motsi na bidiyo. MASHAQATAR TAFKIN KAINJI tana nan a jihohin Neja da Kwara. Akwai ximbin mabambantan halittu a cikinta, waxanda suka haxa da mugun dawa (hippo). Hoton mugun dawa ne ake gani a ruwa. Mashaqatar wuri ne mai qayatarwa, inda mutane ke jin daxin hutawa, a yanayi mai ban sha’awa. Ana gudanar da harkoki da dama da suka haxa da kai-kawon tattakin tafiya da yin sansani ko kallon namun daji. MAGAMA | Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman 11