VURAGUZAN TSOHUWAR DAULAR KEBBI
daga Hamza Shaibu - @officialolobo
Babu sauran nagartaccen gini a wajen alkinta
kayan tarihin duniya na Hukumar Kula da
ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar Xinkin
Duniya (UNESCO), baya ga wata katafariyar
bishiyar kuka. Wannan bishiya dai an ce ta
kai tsawon shekara 500, inda take tsaye cak
a Surame, daxaxxen wajen da ke nuni da
kafuwar tsohuwar Daular Kebbi, wadda Sarki
Muhammadu Kanta ya kafa a qarni 16.
An xauki hotunan valgatattun vuraguzan
abin da ya rage na geffan kusurwoyi huxu
da ke kaiwa izuwa wannan bishiya, wadda ta
12
kasance a ainihin waxannan katangu.
Wannan bishiyar a wancan zamanin ita ce
matattarar ko wajen taron shugabannin/
dattijan al’ummar Surame, inda sukan tattauna
kan yadda za a shawo kan muhimman
matsalolin da ke ci wa al’umma tuwo a
qwarya; a wajen dai ake cimma masaya,
sannan a bainar jama’a ake hukunta masu
aikata miyagun laifuka. Yanzu vuraguzan
Surame an yi watsi da su a Sakkwato, wato
kimnin kilomita huxu daga Qaramar
hukumar Binji. Wannan wuri yana da matuqar
MAGAMA | Nuwamba 2018 Fitowa Ta Musamman
muhimmanci a tsakanin mazaunan karkarar,
saboda suna nuni da tushen asali, sannan sun
samar da muhimmiyar alamar da ke qarin
haske kan yadda magabata suka rayu, tare
da irin gine-ginensu da tsarin rayuwarsu,
al’amarin da ya bunqasa tsawon shekaru.
Kasancewar wajen wurin alkinta kayan
tarihi na Hukumar kula da ilimi da kimiyya
da al’adu ta Majalisar Xinkin Duniya, wato
UNESCO, waxannn vuraguzai suna xaukar
hankalin masu kawo ziyarar gani da ido daga
ko’ina a xaukacin faxin duniya, lamarin da ke
bunqasa tattalin arzikin karkarar.