Magama Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman | Page 10

WADANDA SUKA BIYO BAYANZU DUTSEN OLUMO katafaren dutse ne da ya bulluqo tsawon zamanin. Tarihin Dutsen Olumo ya samo asali ne tun daga qwarin na19 a daular Oyo, zamanin da mutanen Egba suka mamaye Abeokuta, waxanda suka samu mafaka daga mahara a yaqin da aka yi tsakanin qabilu a zamanin. Wannan dutsen ya zama wurinda ke bayar da qwarin gwiwa ga mutanen Egba a zamanin yaqin, kuma mahangar fahimtar ko abokan gaba sun kawo hari. Dutsen Olumo tambarin haxin kai ne da ‘yanci, ba wai ga al’umma Egba kawai ba, har ma ga xaukacin mazaunan Abeokuta da ke Jihar Ogun. s a i h t t Ma ARAGBADA - @dudutoonznigeria Matthias Aragbada ya samu daraja ta biyu a gasar xaukar hotuna ta NaijaGEMs, inda ya shiga gasar da hoto na sama. Ya ziyarci jihohin Najeriya guda takwas yana xaukar hotuna kafin ya cimma matsaya kan hoton da ya dace ya shiga gasar da shi, wato wanda ya xauko daga saman dutsen Olumo, har ta kai ga yana matuqar qaunarsa saboda qarfin tasirinsa wajen nuna daxaxxun al’adu. Abin da ya fi ban sha’awa, shi ne Mathias bai yi hotuna masu yawa da suka nuna jerin tsirrai da furanni. Kodayake kamfaninsa na sarrafa hotuna, wato Dudutoonz ya fi qawata surar hoto sunkutukum (gaba xaya) da xaukar hotunan manyan shugabannin kamfanoni, al’amuran da suka kasance ya fi bai wa fifiko a hada-hadar sana’arsa, kodayake yana da mauqar son kutsawa wasu fannonin. Wannan ne dai dalilin da ya sanya ya tunkari wannan qalubalen kaitsaye da jin sanarwar. Bisa la’akari da wannan yunqurinsa na farko a shiga gasar xaukar hoto sai ya samu kasancewa a rukunin mutane uku da suka fi qwazo, al’amarin da ya sanya qimar 10 darajarsa ta nunka a matsayin ta musamman. A cewars, “wannan ya taimaka wajen qarfafa masa gwiwa, sannan ta sanya na fahimci akwai buqatar in qara motsawa kan hanyar da nake bi wajen xaukar hoto, wato in daina taqaita kaina kan abin da na qware kawai. Kutsawa cikin wasu fannonin da zarta qwarewarsa shi ya bai wa Mista Aragbadaya damar kama harkar xaukar hoto ka’in da na’in. Ya samu karsashi da zaburarwa daga labarin mashahurin mai xaukar hoton nan xan Najeriya, Kelechi Amadi-Obi, wanda Lauya ne ya koma mai fenti, ya kuma koma harkar xaukar hoto. Samun ingantattar na’urar kyamarar Canon EOS 80D, Mista Aragbada ya fara aikin da ya yi wa laqabin daga qasqanci zuwa xaukaka (Dust to Roses). Zai je kan titunan Legas ya samu mutane uku da ke fama da matsanancin talauci, waxanda a shirye suke su bayyana wa duniya labarinsu, sai ya taimaka musu wajen aiwatar da manufar su, ta hanyar hotuna. Ta hanyar wannan aiki, manufar da yake son cimmawa ita ce ya nuna wa masu bibiyar ayyukansa cewa za ka iya samun kyakkyawan abu a ko’ina, har ma a inda ba a zata ba. MAGAMA | Nuwamba 2018 Fitowa Ta Musamman