#NotTooYoungToRun, al’amarin da ya haifar
da gyaran kundin tsarin mulki har ta kai ga an
rage shekarun yin takarar muqaman siyasa don
jan ragamar al’umma, kuma lamarin ya zaburar
da ximbin ’yan takarar da suka fito a matakan
qasa da jiha da qananan hukumomi.
Haka nan, qungiyar qawance jawo kowa-
da-kowa a tafi tare ta IFA ta bai wa dubban
mutanen da ke fama da nakasa damar kaxa
quri’a ta hanyar fafutikar ‘kai wa ga Najeriya –
Access Nigeria Camaign’, har ta kai ga Hukumar
zave ta qasa ‘INEC’ ta fito da takardun quri’un
da suka dace da masu raunin gani (ko makanta)
da raunin ji (ko kurumta da bebantaka)
a matsayinsu na masu kaxa quri’un zave.
Mutanen da musifu (yaqi ko tashintashinar
rikici) ta tarwatsa su daga garuruwansu, su
ma sun kasance wani rukuni da ke tattare da
faxawa haxarin cutarwa, amma sai suka samu
ilimantarwa kan yadda za su kaxa quri’a, tare da
faxakarwar zaburarwa a wasu shirye-shirye da
aka gudanar a wasu jihohi.
“Shirin sauqin isa ga Najeriya – Access Nigeria
Campaign da Hukumar zave ta INEC sun
kafa tarihi,” inji Grace Jerry, Babbar Daraktar
qungiyar qawance ta IFA. “Qimar taimakon
da aka bai wa masu kaxa quri’a da ke fama
da raunin gani (ko makanta) lamari ne mai
matukar ban mamaki da gamsarwa a karon
farko.”
Sauran qungiyoyin da suka taimaka wa masu
kaxa quri’a su fahimci yanayin muhallin da
za su yi zave, sun jawo al’umma ne a jika don
tattaunawa.
Xakin juya akalar al’amura (tattara bayanai/
alqaluma da tantance sahihncinsu) nan ne
wajen fitar da sabon nazarin gyare-gyaren da
aka yi wa Dokar zave, yayin da cibiyar tsare-
tsare da kula da dokoki ta tattara, ta kuma
bayar da qare-qaren da aka yi a kai-a kai na
sauye-sauyen dokokin da suka danganci zave,
waxanda xaukacinsu an tsara ne da manufar
kyautata yadda za a samu nagartar tsare-tsaren
ayyuka. Gidauniyar fafutikar matan Najeriya ta
‘NWTFA’ ta shiga fafutikar ganin ana damawa
da xaukacin matan Najeriya, a matsayinsu
na ’yan takara da masu kaxa quri’a, yayin da
Cibiyar ‘’Yar’adua ta samar da rahotannin
al’amuran da suka faru a xaukacin faxin qasar
ga masu kaxa quri’a da jami’an zave da jami’an
tsaro.
Ma’aikatan tattara bayaanai a Cibiyar bibiyar alqaluman quri’u da sakamakon zave
a kan-kari na qungiyar YIAHGA Africa da suka yi aikin sa’ido a zabukan Fabarairu
Wani babban abin damuwa kafin zave, shi
ne, tunanin tashe-tashen hankula. Wani
bincike da aka gudanar a xaukacin jihohi 36
da Gidauniyar CLEEN, wata qungiyar da ba
ta gwamnati ba, ta gudanar da ke fafutikar
tabbatar da kariya da tsaro da adalci, inda aka
tantance haqiqanin al’amuran da ke iya rura
wutar rikicin zave, kuma an gano “wurare
mafi muni” a xaukacin faxin qasar, inda aka
yi ankararwar gargaxi tashin farko, tare da
ayyukan haxin gwiwar kashe wutar rikici,
musammamn a yankin Arewa maso Gabas
da ya yi fama da rikice-rikice (tashin tashinar
Boko Haram) da yankin tsakiya.
Don shawo kan tashe-tashen hankula kafin
aukuwarsu, sai aka fara kiraye-kiraye ta kafar
sadarwa da laqabin #Vote Not Fight peace- Yi
zave ban da faxa a zauna lafiya’ a qarqashin
jagorancin mai wasan nishaxantarwa da
fafutikar kyautata rayuwa, “2baba”Idibia da
cewa, ‘A daina tashin hankalin keta haddin
mata a siyasa’ qarqashin jagorancin jarumar
fina-finai Stephanie Okereke Linus, wadda
ta yi ta kiraye-kirayen dakushe tashe-tashen
hankula da tabbatar da zaman lumana, tare da
kyautata yanayin jawo matasa a dama da su,
yin zave cikin lumana da shigo da mata cikin
tafiyar a dama da su.
Duk da cewa an samu matsalolin da ba za a iya
shawo kan su ba, haxakar qungiyoyin fafutuikar
haqqoqin al’umma a Najeriya sun tabbatar da
cewa, suna da matuqar muhimmanci a qoqarin
da ake yi wajen tabbatar da kafuwar qaqqafar
dimokuraxiyya, har zuwa qarshen zavukan da
qasar ta gudanar a shekarar 2019. Ta hanyar
jajircewa wajen tursasawar ganin an aiwatar da
gyare-gyaren siyasa da faxaxa fagen bai wa ’yan
qasa damar shigowa harkokin siyasa, ta yadda
kasancewarsu zai yi tasirin tabbatar da gaskiya
qeqe-da-qeqe, tare da xaukar xawainiyar
sauke nauyin al’umma da ke rataye a wuyan
gwamnati.
Tallafawa da goyon baya ga tsare-tsare da
cibiyoyin hada-hadar harkokin siyasa da sake
fasalin zave, ta hanyar faxaxa fagen jawo
kowa-da-kowa a cikin tsare-tsaren harkokin
zaven, ta yadda qungiyoyin fafutikar haqqoqin
al’umma za su tabbatar cikar nagartar zavukan
shekarar 2019. Nasararsu ta qarfafa, ta yadda
qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma masu
cin gashin kansu za su iya shigowa harkokin
zave a dama da su nan gaba.
Ta hanyar jajircewa wajen tallafa wa tsarin
gudanarwa da cibiyoyin harkokin siyasa da
gyaran zave, wajen faxaxa fagen jawo kowa-
da-kowa a tsarin gudanar da zave, sannan
qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma su
samu cikakkiyar nagarta a zavukan shekarar
2019. Nasararsu na qara qarfafa sanadiyyar
shigowar qungiyoyin fafutikar haqqin al’umma
masu cin gashin kansu, ta yadda za a tafi tare a
wajen gudanar da zavukan da za a yi nan gaba
a Najeriya.
Taron manyan jami’an gudanarwar qungiyar YIAGA Africa, qarqashin jagorancin Hussaini Abdu (na uku daga dama) yayin da yake ganawa da ’yan jarida
a ranar zave, a can daga gefensa Jakadan Amurka ne, W. Stuart Symington (can daga dama) da Jakadan Birtaniya Catriana Laing (can daga hagu)
8
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019