DANGANTAKAR AMURKA DA NAJERIYA
BAYAN ZAVE
WANE LAMARIN ZA A SHIGA?
Daga Sani Mohammed
M
anyan zavukan shekarar 2019 su ne
karo na shida da aka gudanar tun
bayan da qasar ta dawo kan tafarkin
dimokuraxiyya a shekarar 1999. Bayan
hakan xaukacin masu zave da waxanda aka
zava dole su qudure cewa shiga hada-hadar
zave ya fi gaban kaxa quri’a ko tsayawa
takarar zave.
Muhimmiyar manufar qarshe da za a
cimmawa a takarar siyasa ita ce gina qasa,
inda managarta xaixaikun ’yan qasa da
hukumomi za su mayar da hankali kacokam
wajen tabbatar da jagoranci nagari; ta
yadda majalisa da kotuna za su hana keta
haddin qarfin iko, su kuma tabbatar da cewa
harkokin mulki sun daidaita kan doron
tabbatar da adalci qarqasin bin qa’idojin
doka; a inda shigowar farar hula ke qarfafa
ikon mutane.
A xaukacin faxin duniya babu wani zave
mara illa. Sai dai dole ne kowace qasa ta yi
qoqarin kawar da yawan matsalolin da ke
kawo cikas xin gudanar da managarcin zave
na adalci, yin gaskiya qeqe-da-qeqe da ke da
qimar nagartar da za a aminta da shi, tare da
gudanar da zaven cikin lumana, wanda zai
kasance cimma manufar mutane ne da ke
xamfare da burin kafa dimokuraxiyya.
Sharhi kan tsarin dimokuraxiyyar Najeriya
a wani kundi da aka wallafa a shekarar 2013,
Hukumar Majalisar Xinkin Duniya da
ke kula da bunqasa Rayuwar Al’umma ta
UNDP, ta yi nuni da cewa, “Idan a haqiqanin
gaskiya jami’an hukuma da aka zava ba sa
jin cewa suna da wani nauyi da ya rataya
kan muqaminsu da lallai sai sun sauke shi
za su kyautata wa waxanda suka zave su, to
da wuya su xauki muqaminsu a matsayin
dalilin jan ragamar al’umma.” A kan qarke
da cewa “Idan masu riqe da muqamai ba
su da tabbacin cewa waxanda suka zave
su za su bi kadin yadda suka sauke nauyin
da ya rataya a kansu ko ya suka tafiyar
da muqamansu, to abin da ya sha musu
gaba (sha’anin gabansu) kawai za a gani ya
bayyana.”
Majalisar Xinkin Duniya ta bayyana cewa
shugabanci ko jagoranci nagari ana auna
qimarsa ne bisa matakai takwas da ake tafiya
kan doronsu, wato qa’idar doka da gaskiya
qeqe-da-qeqe da yarjejeniya fahimta da
matsayar daidaito da daidaiton adalci, tare
da shigowar kowa-da-kowa, tattare da qarin
qaimi da nagarta da sauke nauyin da aka
xora wa zavavvun masu riqe da muqamai.
Waxannan qa’idoji su ne xaukacin qasashen
da ke biyayya ga qudurin Majalisar Xinkin
Duniya suka tabbatar da su (ko rattaba
hannu kan su).
• Shigowar al’umma lamarin na buqatar
xaukacin qungiyoyi, musamman
rukunin mutanen da ke tattare da
haxarin rayuwa sun samu shiga
kaitsaye ko wakilcin da zai ba su damar
isa ga gwamnati. Wannan na faruwa
ne idan aka samu qaqqarfar qungiyar
fafutikar haqqoqin al’umma da ’yan
qasa da ke da ’yancin walwala da
bayyana ra’ayinsu.
• Bin doka ana doka misali ne a aikace
ta hanyar rashin yin katsalandan a
tsarin dokokin da ke bayar da kariya
ga ’yancin xan Adam, tare da tabbatar
da haqqoqin fararen hula ’yan qasa,
musamman ’yan tsiraru (qabilu ko
mutanen da ba su da yawa). Ana
tabbatar da hakan ne ta wajen samar da
hukumar da ke jan ragamar doka mai
cin gashin kanta da jami’an ’yan sanda,
waxanda ba su xamfaru da cin hanci da
rashawa ba.
•
•
Gaskiya qeqe-da-qeqe na nufin cewa
’yan qasa suna da fahimta, kuma suna
iya kaiwa ga hukumomi da dabarun
yanke matsaya kan al’amuran da
suka shafe su, musamman idan irin
al’amuran da aka cimmawa sun shafe su
kaitsaye. Dole ne a samar da waxannan
bayanai ta yadda za a fahimta, tare da
samar da su cikin sauqi, wato a yaxa su
a kafafen yaxa labarai.
Xaukar mataki wannan lamari na
tattare da nuna yadda hukumomi ke
xaukar mataki kan abin da ya shafi
masu ruwa da tsaki (al’umma) kan kari,
wato cikin lokacin da ya dace.
• Yarjejeniyar fahimtar juna ita ma
manufa ce da ke nuni da qudurin
da ke samar da masalahar daidaito
a tsakankanin ximbin buqatu da
fahimta iri-iri da burin ximbin ’yan
qasa mabambanta. Ana yanke matsaya
ne kan buqatu bisa doron cikakkiyar
fahimtar tarihi da al’ada da tsarin
zaman tare a al’umma.
• Daidaiton adalci da jawo kowa-da-
kowa a jika ya dogara ne kan yadda ake
tabbatar da cewa xaukacin mutanen
da ke cikin al’umma sun ji cewa ana
yi (tafiya) tare da su, kuma an tallafa
musu don halin rayuwarsu ya inganta,
musamman xaixaikun mutane da
rukunin waxanda ke tattare da aukawa
haxarin cutuwa a rayuwa.
• Tasirin nasara da nagarta ana
bunqasa yanayin ne ta hanyar xorewa
wajen kyakkyawan amfani da ximbin
albarkatu don biyan buqatun al’umma.
Xorewar al’amura na nufin xaukacin
tallafin bunqasa rayuwa da ake bayarwa
da albarkatun qasa da ake ririta su, ana
alkinta su don amfanin al’ummar da ke
tasowa
• Bin kadin sauke nauyi na nufin
hukumomi ana tuhumarsu, inda
mutane ke yin kyakkyawan bin kadin
sauke nauyin mutane a tsakanin kowa
da kowa. Lamarin ya haxa hukumomin
gwamnati da qungiyoyin fafutikar
haqqoqin al’umma da kamfanoni masu
zaman kansu duk sai an bi kadin sauke
nauyin al’umma da ya rataya a kansu.
Xaukacin waxannan al’amura da ake ta
kai-kawo a kan su, an tattaro su ne don
buqatar da ake da ita ta shugabanci nagari,
wato manufar ita ce daidai lokacin da aka
kammala manyan zavuka – sai a jajirce
wajen aiki tuquru don gina qasa.
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
9