dimokuraxiyya a Najeriya
Mai rubutu Olufunke Baruwa | Gudunmuwar hoto YIAGA
A
lokacin zavukan 2019, qungiyoyin
fafutikar haqqoqin al’umma (CSOs),
tare da tallafin Hukumar Raya Ci
gaban qasashe ta Amurka ‘USAID’ shi
ne al’amarin da ya bayar da damar shigowar
qungiyoyin fararen hula da masu sa’ido kan
harkar zave na cikin gida, tare da kawar da duk
wani tarnaqin tayar da rikici. Sun tabbatar da
cewa su turaku ne masu qarfi da Najeriya za ta iya
dogara da su a matsayin managartan muryoyin
da za su tabbatar da cewa gwamnati ta sauke
nauyin alqawuran da ta xauka wajen gudanar da
tafarkin dimokuxariyya da bin qa’idojinta.
Qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma sun
tattaro ximbin masu sa’ido a harkar zave na
cikin gida a Najeriya, waxanda ba a tava samun
kwatankwacin yawansu ba, tun bayan da qasar
ta koma mulkin farar hula cikin shekaru ashirin
da suka gabata. Hukumar Zave ta qasa (INEC) ta
tantance qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma
na cikin gida 120 da rukunin masu sa’idon
harkokin zave ‘yan qasashen waje 36, inda suka
samar da ‘yan aikin sa’ido kimanin dubu bakwai
da xari uku (7,300).
Da aka fara hada-hadar ayyukan zave, waxannan
rukunin mutanen sai suka haxa qarfi wajen
zaburar da al’umma kan lallai su fito su kaxa
quri’unsu a wajen zave, masu fafutikar yaxa
manufofin dimokuxariyya, sannan su bayar da
rahoto kaitsaye kan yadda al’amura ke gudana a
haqiqanin lokacin lura da abin da ke faruwa, su
kuma su baza a kafafen sadarwar intanet na sada
zumunta da sauran kafofi.
Cynthia Mbamalu (a dama), Manajar
Shirin YIAGA Africa ke bayanin bibiyar
tattara sakamakon zave a Cibiyar nazarin
sakamakon ga Tsohuwar Shugabar Laberiya,
Ellen Johnson Sirleaf (a tsakiya), shugabar
ECOWAS wajen sa’ido a kan zaven Najeriya,
tare da Jami’ar gudanarwar YIAGA, Aisha
Abdullahi (a hagu)
An vullo da ximbin dabarun sa’ido kan
harkokin zave, tare da samar da rahotanni
daga qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma
da suka bayyana yadda zavukan shekarar 2019
suka kasance. Waxannan (dabaru) sun haxa da
qimanta nagarta ‘xakin tattara bayanai’ wajen
nazarin yadda harkokin za su wakana tun kafin
a gudanar da zaven, sannan su bi kadin yadda
ake yin zave a haqiqanin lokacin da aka fara;
musamman al’amarin da ya shafi kafa mahangar
‘dangantakar jinsuna da zave’ da ‘tattara
alqaluman zave’ ta yadda za a samu cikakkun
bayanai/alqaluma a haqiqanin lokacin da aka
gudanar da zave; kuma an samar da rukunin
haxakar mutanen da aka tura dubbai ’yan qasa
da ke aikin sa’ido; da tattara bayanai da nazarin
tantance xaukacin bayanan da aka samu daga
masu kaxa quri’a da jami’an tsaro da jami’an zave
da ’yan takara.
A haxin gwiwar tsawon lokaci da qungiyoyin
duniya da ke kula da harkokin zave irin su ‘IFES’
da cibiyar ‘IRI’ da cibiyar dimokuraxiyya ta ‘NDI’,
inda Hukumar raya ci gaban qasashe ta Amurka
‘USAID’ ta tallafa wa manyan qungiyoyin
fafutikar haqqoqin al’umma na qungiyoyin da
ba na gwamnati ba, waxanda daga cikinsu suka
haxa da YIAGA Africa, wada ta gudanar da
nazarin zuba alqaluman quri’un da aka kaxa bisa
tartibin alqalumanta na ‘PVT’ don tabbatar da
qimar sakamakon zaven da jami’an hukumar
zave suka bayyana wa al’umma.
Kafin ranar da za a gudanar da zave, qungiyar
YIAGAAfrica mai fafutikar tattabatar da
dimokuraxiyya da haqqin xan Adam a Afirka
ta kawo masu aikin sa’ido kan harkokin zave
fiye da 3,000 a xaukacin faxin qasar nan da
suka karaxe qananan hukumomi 774, sannan
suka gudanar muhimmiyar zubeben qwarayar
alqaluman quri’un da aka kaxa bisa ma’aunin
‘PVT’ lokutan xaukacin zavukan shugaban qasa
da na ’yan majalisar qasa. To kafin zaven dai
qungiyar YIAGAAfrica mai fafutikar tabbatar da
dimokuraxiyya da ’yancin xan Adam a Afirka
ta sanya ximbin masu sa’ido a harkar zave na
tsawon lokaci, inda suka tantance kyautatuwar
yanayin muhali da shirin zave, har ta kai ga sun
yi hasashen al’amuran da za su iya wakana ko
faruwa ranar zave da bayan kammalawa.
Don tattara alqaluman tantance sahihancin zave
bisa ma’aunin ‘PVT’ rukunin masu aikin sa’ido
sun tattaro samfurin bayananan/alqaluman daga
fiye da rumfunan zave 1,500 a xaukacin kowace
qaramar hukuma ‘Duban quri’a’ a cibiyar tattara
bayanai ta qasa a tsarin ‘qidayar sauri/hanzari’
wajen fitar da jaddawalin alqaluma. Qimar
ma’aunin zinaren masu aikin sa’ido kan harkokin
zave ’yan qasa, tare da qirgar hanzari ta masu
cin gashin kansu (ko yin aiki a qashin kansu) su
aka yi amfani da su wajen auna ingancin a ranar
zave da sakamakon da aka fitar, al’amarin da ya
tabbatar da nagartar sakamakon Hukumar zave
ta qasa ‘INEC’ ta bayyana.
“Idan har babu tallafin Hukumar Raya ci gaban
qasashe ta Amurka ‘USAID’ irin waxannan
dabarun ba za su kai ga nasarar kafa qungiyoyin
da ke da rajin kare qasa ba,” a cewar Cynthia
Mbamlu, manajar shirin ayyukan qungiyar
YIAGAAfrica. “’Yan qasa sun samu cikakkiyar
fahimtar zavuka da tsare-tsaren gudanarwa fiye
da yadda al’amura suka kasance a baya.”
Kafin dai a gudanar da zaven, Hukumar
USAID ta tallafa wa qungiyar fafutikar
haqqoqin al’umma da laqabin fafutika na
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
7