RAHOTON ZAVE
Mahangar mai
sa’ido a harkar zave
Daga Temitayo Famutimi
R
ichard hamshaqin mai hada-hadar
kaddarorin gidaje da filaye ne
da ke zaune a Legas. Ya yi tafiya
zuwa qauyensu da ke Qaramar Hukumnar
Aniocha ta Arewa da ke Jihar Dalta
kafin zaven Shugaban qasa da aka tsara
gudanarwa a ranar 16 ga Fabrairu. Cikin
zaquwar farin ciki, har ta kai ga ya kasa
yin barci a daren 15 ga Fabrairu. Ya farka
da safe sai ya ji labari mai tayar da hankali;
kimanin sa’ao’I biyar ya rage a fara gudanar
da zave sai Hukumar Zave ta qasa (INEC)
da ke da alhakin gudanar da zaven ta bayar
da sanarwar xage zave zuwa mako guda.
Richard ya ji takaicin jin cewa an xage
zaven. Duk da haka sai ya qara wa’adin
zamansa a qauye zuwa makonni uku don
tabbatar da cewa an yi zavukan da shi, wato
wanda aka xage na shugaban qasa da na
gwamna da ke qaratowa.
“Ban tava fashin yin zave ba tun bayan
da Najeriya ta dawo mulkin farar hula
cikin shekarar 1999. A gaskiya, saboda
haka wannan shekarar ma ba zan qi yi ba,”
kamar yadda ya bayyana mini.
Richard na xaya daga ximbin ’yan Najeriya
masu kishin qasa waxanda suka yi takakka
zuwa xaukacin faxin qasar don a yi zave
tare da su. A gaskiya, akwai rahotannin da
ke nuna cewa ’yan Najeriya daga nahiyar
Arewacin Amurka da Turai da Asiya sun
dawo qasar don shiga a yi zavuka tare da
su.
Cike da zaquwa tare da son a aji su, Richard
da sauran mutanen karkarar sun halarci
rumfunan zave tun wajen qarfe 6:30 na
safe. Sai dai kayan zave da jami’ai duk ba su
zo wajen ba har zuwa qarfe 8:15 na safe. An
dai fara yin zaven wajen qarfe 9:10 na safe.
A xaukacin faxin qasar ’yan qasa sun
jajirce wajen ganin sun yi amfani da damar
’yancinsu na kaxa quri’unsu.
4
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
A Asaba babban birnin Jihar Dalta, ba a
fara yin zave ba a wurare da dama har zuwa
qarfe 11 na safe. Can kuwa a Firamaren
Uzoigwe, wata Cibiyar yin rajista mai xauke
da rumfunan zave kimanin 12, xaruruwan
masu kaxa quri’in sun yi takaicin
makararar da aka yi na fara zaven. Ximbin
na’urorin tantance katunan zave (Card
Readers) ba sa aiki. Da yawan masu zave
sun harzuqa, xaukacin matasa da tsofaffi,
an gan su suna ta neman masu aikin sa’ido
na cikin gida da waxanda suka zo daga
qasashen duniya, don su nuna musu rashin
jin daxin su (kan lamarin da ya faru).
Wani mutum ya yi ihu da furta cewa “Babu
wanda zai bar wurin nan har sai dukkanmu
mun kaxa quri’unmu.” zaman lafiya. Kwanaki biyu kafin zaven
gwamnoni, sarakunan gargajiyar Sagamu
sun yi al’adun addinin gargajiya iri-iri
don tabbatar da nasarar wajen tsoratar da
miyagun mutane da masu yunqurin satar
akwati da masu tayar da rikici.
Duk da makarar da aka yi wajen fara zaven,
al’amarin da ya kawo cikas na kashin farkon
zavukan 2019, ’yan Najeriya sun nuna
muhimmancin zaven gwamnoni da ’yan
majalisar jihohi, inda aka samu qaruwar
waxanda suka fito don kaxa quri’unsu in
an kwatanta da waxanda suka fito zaven
shugaban qasa. Ana ganin gwamnatocin
jihohi a matsayin gwamnatin da ke yin
tsare-tsare masu tasiri a rayuwar yau da
kullum ga mafi yawan ’yan qasa. Duk da haka an samu ximbin matsaloli da
suka haifar da cikas ga nakasassu da tsofaffi
tukuf-tukuf, domin rukunin irin waxannan
mutanen sun kasa isa waxannan rumfunan
zave. Babu quri’un zaven da aka tanada
don makafi, ko tabaron kambama hotuna
ga mutumin da idanunsa ba su da qarfin
gani a ximbin rumfunan zave da ke jihohin
Ogun da Dalta.
A xaya daga rumfunan zaven da ke
Qaramar Hukumar Sagamu ta Jihar Ogun,
masu kaxa quri’u sun qanqame kujerun
wata makarantar elemantare da ke kusa
da wurin, inda suka jeru kan layi a zaune.
Duk suna riqe da lema don kare kansu
daga zafin rana. Wurin zaven dai ya nuna
a natse ake, amma dai akwai jami’an tsaro.
Da yake an fafata zaven gwamna mai zafi a
jihar, sarakunan gargajiya sun yi matuqar
taimakawa wajen tabbatar wa al’umma da
muhimmancin zaman lafiya.
Tawagarmu ta fahimci cewa muhimman
sarakunan gargajiya sun yi taro a xakin
taro, tare da talakawansu inda suka buqace
su da su bai wa Hukumar zave ta INEC
haxin kai da ’yan sanda don tabbatar da
A rumfar zaven da ke Qaramar Hukumar
Ikenne a Jihar Ogun, wani mataimakin
jami’in gudanar da zave an hango shi
yana taimaka wa wani tsoho mai shekara
tamanin bayan da ya kammala kaxa
quri’arsa a matsayinsa na xan qasa. An
hango mata masu juna biyu da masu
nakasa da aka ba su fifikon muhimmanci
wajen ba su damar kaxa quri’a a rumfunan
zave da dama da ke faxin yankin.
Daidai lokacin da aka kammala zaven
2019, akwai buqatar a yi kyakkyawan nazari
kan yadda aka gudanar da zavukan. Tashe-
tashen hankula da aka samu ba ta kamata
a yardar da aukuwarsu a qasar da ake da
wayewar kai ba, sannan a yi tur da su a
matsayin abin qi. Ta fuskar sufuri da horar
da ma’aikatan zave da dogaro da takardun
quri’un da ake jefa wa akwati da tsarin tsaro
– xaukacin waxannan al’amura xaya bayan
xaya sai an yi musu cikakken nazari.
Sannan zai yi matuqar fa’ida ga Hukumar
zave ta qsaa INEC ta bibiyi irin
shawarwarin da masu aikin sa’ido a zave na
cikin gida da ’yan qasashen waje suka bayar
don inganta tsarin gudanar da zavuka nan
gaba. Najeriya bai kamata ta bari a ci gaba
da maimaita mtsalolin da aka fuskanta a
zaven 2019 ba, don ka da su sake aukuwa.