SAQON JAKADA
Najeriya a lokacin manyan zavukan shekarar
2019 da aka kammala ba da dadaxewa ba.
Mun bayar da horo da ayyukan sa’ido, tare
da bin kadin al’amuran da suka wakana,
sannan mun yi aikin haxin gwiwa da
qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma
don tabbatar da gaskiya qeqe-da-qeqe ta
yadda za a kauce wa tashin hankali. Kamar
yadda muka sha bayyanawa, muna tallafa wa
tsarin dimokuraxiyya, ba wai xan takara ko
jam’iyya ba.
W. Stuart Symington
Jakadan Amurka a Najeriya
Maraba da fitowar sabuwar Magama
Mun haxu xamfare da tunani irin na
xaukacin ’yan uwan da suka jajirce wajen
fafutikar kafa dimokuraxiyya, tattare da
’yancin da dimokuraxiyya ta ba mu na
zaven shugabanninmu. A wannan fitowar za
mu bibiyi wasu daga hanyoyin da Ofishin
Jakadancin Amurka a Najeriya ke motsa
ruhin dimokuraxiyya a cikin al’ummar
MAGAMA
Ana wallafa ta ne a bayan kowane wata
uku a sashen Hulxa da Jama’a na Ofishin
Jakadancin Amurka a Najeriya
TAWAGAR EDITOCI
Aruna Amirthanayagam
(Mai Bayar da Shawar kan Hulxa da Jama’a)
Russell Brooks
(Jami’in Hulxa da Jama’a a Legas)
Glenn Guimond
(Jami’in Aikin Jarida)
Olaoluwa Aworinde
(Edita da Daukar Hoto)
Xaukacin sakonni a aike ta
wannan adireshi:
Ga Editan, Mujallar Magama
Sashen Hulxa da Jama’a na Ofishin
Jakadancin Amurka
Plot 1075 Diplomatic Drive,
Central Business Area, Abuja, Nigeria
Tel: (09) 461-4000. Fax: 09-461-4305
OFISHIN LAGOS:
Ofishin Jakadancin Amurka
2, Walter Carrington Crescent, Lagos
Tel.: +234-703-150-4867/2444
E-mail: [email protected]
Website: ng.usembassy.gov
A biyo mu ta:
A babban labarin da muka kambana
a gaban mujalla, mun yaba da murnar
gwarzantakar Abdullahi Abubakar, wani
limami mai qanqan da kai da ke jagoranci a
kan tsaunukan da ke Jihar Filato. Za ku ga
yadda limamin ya ceto rayukan xaruruwan
Kiristoci makwaftansa. Jajircewar limamin
na nuni da irin hangen nesansa da ke nuna
’yan uwantakar juna a tsakaninmu. Ya hau
doron kirarin qasar Amurka, manufar son
Amurka a zuci: Daga mafi yawa, guda ce.
Wannan manufa ta bijiro da qarfinta a
Najeriya tamkar yadda ta kasance a kowane
wuri da ke doron qasa. Abin da ke zaburar
da shi a rayuwa; labarinsa managarcin
al’amari ne da ke nuni da gaskiyar da babu
shakku a cikinta kan cewa muna buqatar
kulawa da xaukacin junanmu, sannan mu
vullo da mafita ga kowane mutum, ba tare
da la’akari da harshen da muke magana
da shi ba; ko inda muke yin ibada; ko
jinsunanmu, ko wane ne muke qauna, ko ma
sana’ar da muke yi don samun abin gudanar
da harkokin rayuwa.
Kuma mun bayyana bukukuwan da muka
gudanar cikin watan Tunawa da tarihin
baqaqen fata da aka yi cikin watan Maris.
Qasar Amurka a kullum ta himmatu wajen
bunqasa rayuwar xan Adam a Najeriya,
kuma babu wani fanni da ya fi fa’ida wajen
zuba ximbin kuxi fiye da fannin lafiya. Don
haka sai a duba ximbin bayanan da ke ciki
kan yadda muke tallafa wa Najeriya wajen
bin kadin manuniyar qanjamau/cuta mai
karya garkuwa jiki, tare da nazarin tasirinsu
(NAIIS). Wannan shi ne mafi girman
bincike da aka tava gudanarwa a faxin
duniya. Sakamakon ya nuna irin nasarar
da aka samu wajen yaqi da wannan cuta a
wurare da dama, tare da inda aka samu givi
ko naqasu ta yadda za mu qara qaimi wajen
kawo qarshen annobar cutar qanjamau a
Najeriya.
Waxannan labarai da sauran al’amura na
jiranku ku bibiyesu a shafukan da ke biye da
juna. An tattara su gaba xaya, don haka ina
ganin hujjoji ne a bayyane qarara da ke nuna
nasarar da muka samu wajen yin aiki tare
don kyautata makomar rayuwa ga xaukacin
’yan Najeriya dangane da Kyautata ci gaban
rayuwa a Najeriya kan doron abin da aka
tsara daga Amurka.
Aji daxin karatu
W. Stuart Symington
A wannan fitowar...
Vol. 25 No. 1
Rahotannain Sa’ido
kan zave Gudunmuwar
YALI
Shafi na 4 Shafi na 12
Dimokuraxiyyar
Najeriya
Shafi na 6
Bayan zave: Me za a
tunkara? Shafi na 9
Babban
Labari
Shafi na 10
Gidauniyar
Aspilos
Shafi na 13
Manuniyar NAIIS
ta shekarar 2018
Shafi na 14
Watan Tarihin
Mata
Shafi na 16
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
3