EducationUSA
MAHANGAR MATASHIN QARNI
NA 21 KAN MANYAN ZAVUKA
Daga Moses Okoye
ewar an yi zave kawai tamkar ba a ce
komai ba ne. A ranar 23 ga Fabrairu,
’Yan Najeriya ba wai fita kawai suka
yi don kaxa qui’a ba, har ma a iya
cewa sun fito ne domin a ga irin tasirin
qimar su, tare da bayyana ra’ayoyinsu ta
yadda suka danqa qasar a hannun mutanen
da suke ganin nagartarsu wajen ciyar da
qasar gaba. Kuma wani tsukukun qaqa-ni-
ka-yi ne da ’yan Najeriya suka shiga ba tare
da la’akari da bambance-bambancen da ke
tsakaninsu ba, inda aka tattaro su, aka ba su
qarfin ikon bai-xaya don su ne masu yanke
matsaya. A taqaice ta kasance rana ce ta ’yan
Najeriya a cikin qasar.
C
Na kasance xaya daga cikin waxanda
suka shiga shirin Asusun bayar da dama
qarqashin Baje-kolin ilimi na Education
USA a ofishin Jakadancin Amurka da
ke Abuja, Najeriya cikin shekarar 2017,
kuma gogewata zuwa yanzu ta kasance ta
ilimantarwa ce, tamkar yadda ta kasance ta
buxe ido ce. Ba wai kawai mafitar warware
matsaloli da samun dama a wuraren da a da
nake ganin cikas (xin rayuwa), har ma na
gano tasirin ingantacen ilimi wajen warware
matsalolin da suka yi kiki-kaka (aka kasa
shawo kansu). Don haka a zavukan 23 ga
Fabrairu, lamarin ya zamo jiki a gareni
wajen karkata ga xan takarar da ke da
himma wajen inganta ilimi a xaukacin
faxin qasar nan, sannan ya bayar da fifikon
kulawa ga mutanen da suka haxa da xalibai
da qananan ’yan kasuwa (’yan tireda) da
18
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
ma’aikata a ofisoshi (na gamnati ko masu
zaman kansu).
Muhimman matakai da Hukumar Zave ta
qasa (INEC) da gwamnatin Najeriya suka
xauka don shirin zavukan qasa don shirya
wa manyan zavukan qasa. Rumfunan zave
sama da 154,000 aka tanada a xaukacin
faxin qasar da manufar sauqaqe yin zave.
’Yan Najeriya masu yi wa qasa hidima
(NYSC) su ma sun bayar da gudunmuwarsu,
inda aka tura ’ya’yanta, waxanda suka jajirce
wajen gudanar da ayyuka ba a ma a birane
ba, har ma da surquqin wuraren da ke da
wahalar shiga a yankunan karkara. Jami’an
tsaro ma ba a bar su a baya ba, a wajen
wannan aiki. Mutanen da ke sanye da kayan
sarki fiye da 500,000, waxanda suka haxa
da jami’an ’yan sanda da soja da sojojin
sama da jami’an sojan ruwa duk an tura su
ko’ina a faxin qasar nan. Wani na iya kai-
kawo a tunani kan dalilin da ya sanya aka
xauki waxannan ximbin matakai don wani
al’amarin da za a yi rana guda. Ko an yi ne
don tabbatar da cewa ayyuka sun gudana ba
tare da wata matsala ba, yadda za a kauce
wa danniya da murxiyya (aringizo ko satar
quri’u); wani tsari da xan/’yar Najeriya ke
da ta cewa a cikinsa a haqiqanin abin da ya
shafi jan ragamar shugabancin qasarsa/ta?
Idan kuwa haka ne, to waxanne nasarori irin
waxannan matakan suka yi tasirin cimma
wannan manufa?
Tsarin gudanar da zave, na fahinci cewa
tamkar abincin da ya fi dacewa a zubo shi
ne da zafinsa xungurungum lokacin da
yake tururin fitar da qamshi, a zuzzuba a
farantai masu tsafta, sannan wanda ya fi iya
girki ne zai rarraba. Kawai dai tamkar yadda
wanda zai ci abinci ba shi da ta cewa game
da abinci da mai girki ya sarrafa ya girka,
jagororin qasar ba su da ta cewa a kan zavin
mai kaxa quri’a a ranar zave. Ranar zave a
gareni, rana ce da mutumin da ba kowa ba
ke haskakawa, kuma duk wani yunqurin
dusashe haskensa zai haifar da keta doka.
Yayin da muka yunqura a matsayinmu na
’yan qasa, sai mu xan tsagaita na kwana guda
ko ma zuwa shekaru huxu, mu bibiyi kadin
badaqalar zave da aka tafka a baya, sai mu
haxa qarfi wajen inganta su a zavukan da za
a gudanar nan gaba. Don qarfin ikonmu ne a
matsayinmu na mutane.
Shirin baje-kolin ilimi na Education USA
a cibiyoyinsa da ke Abuja da Legas yana
bayar da nagartattun bayanai nan take,
waxanda babu naqasu a tattare da su,
dangane da karatu a manyan makarantun
Amurka da aka tabbatar da nagartarsu ga
mutanen da suke hanqoron yin karatu a
qasar Amurka. Don qarin bayani game da
shirin baje-kolin ilimi na Education USA
da damar yin karatu a qasar Amurka, sai a
ziyarci: http://www.educationusa.state.gov