28 ga Fabrairu | Xakin Taro na NUC, Abuja
Wasan Dave (Dandamalin Wasan Kwaikwayo)
Bayan taron tattaunawar sai aka gudanar da wasan dave
(wasan kwaikwayo) na Jeff Stetson mai taken Taron
Tattaunawa – ‘The Meeting’ (1987), wanda aka gina
jigonsa kan hasashen ganawa tsakanin Malcolm X da
Dokta Martin Luther King Jr – tare da haxin gwiwar
sashen wasannin dandamalin dave da fasasohi na
Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. A lokacin wata ganawar
sirri a xakin saukar baki na otal xin Harlem, Malcolm
X da Martin Luther King Jr suka tafka muhawara
kan yadda suka sha bamban da juna a dabarunsu na
kyautata rayuwar Amurkawa ’yan asalin Afirka a cikin
al’ummar da mafi rinjayenta fararen fata ne.
Dokta Jamila Shu’ara
ce ke yi wa xalibai
jawabi a wajen taron
AbdulAziz Attah da Nathan Kure, waxanda suka fito a matsayin Martin Luther King
Jr da Malcolm X lokacin was an wasan dave
28 ga Maris | Ofishin Jakadancin Amurka,
Abuja
Shirin Jawabi
Shirin Baje-kolin ilimi na EducationUSA a Abuja ya
karvi baqwancin tsohon xalibin Jami’ar Howard (da
tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar ilimi), Dokta
Jamila Shu’ara a bikin watan tarihin mata na wannan
shekarar. Dokta Shu’ara ta yi jawabi, inda ta yi bayani
game da buqata da ake da ita ta ilimin ’ya’ya mata
da tallafa wa rayuwar mata. A jawabin nata, ta jawo
hankalin kan irin halin da ta samu kanta lokacin
da take karatu a Amurka, tare da yadda ta samu
shiryarwar dabarun tunkarar qalubalen jagoranci a
muqaman da ta riqe a matsayinta na mace.
WATAN TARIHIN MATA
Fakkriyyah
Hasheem
xaya daga
cikin masu
tattaunawar
ce gabatar
da jawabi ga
masu saurare
6 da 14 ga Maris | Ofishin Jakadancin Amurka, Abuja
Tace Fim da Taron Tattaunawa
Ranakun 6 da 14 ga Maris PAS ta xauki nauyin taron tattaunawa
kan al’amarin da ya shafi keta haddin yin lalata da mata a
kwalejoji da dabarun yadda za a shawo kan matsalar. Mahalarta
taron sun haxa da Fakkriyya Hasheem (Wadda ta kafa qungiyar
fafutikar Amurka ta Arewa Me Too Movement); da Dorothy
Njemanze (Wadda ta kafa Gidauniyar Dorothy Njemanze);
da Dokta Ganiyat Adeshina Uthman (Shugabar Tsangayar
Kimiyyar nazarin zamantakewar al’umma da ke Jami’ar karatu
a wajen makaranta ta NOUN; da Dokta Ekundayo Ocholi
(Daraktar Cibiyar nazarin kariyar tsaron jinsi da bunqasa
matasa (na GSSYA).
4 ga Afrilu | Ofishin Jakadancin Amurka, Abuja
Tattaunawa Kan Keta Hadin Lallata da Mata
Ranar 4 ga Afrilu, mahalarta taron tattaunawa kan keta
haddin lalata da mata a wajen aiki,” da Sashen Hulxa da
Jama’a na Ofishin Jakadancin Amurka ya shirya, ya bijiro da
buqatar inganta dokokin bai wa ma’aikata kariya daga keta
haddin lalata lokacin da suke fafutikar neman abin gudanar
da rayuwa. Rukunin masu tattaunawar sun haxa da Kay
Crawford (Qwararriyar mai bayar da shawara daga Ofishin
Jakadancin Amurka); Joke Aliyu (Abokiyar haxin gwiwa ta
Aluko & Oyebode); da Hansatu Adegbite (Babbar Daraktar
WINBIZ)
Jarin masu tattaunawa a taron: Hansatu Adegbite na jawabi
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
17