WATAN TARIHIN BAQAR FATA
25 ga Fabrairu | Rediyon Jami’ar Legas
Bayana a Shirin Rediyo
Jami’in Hulxa da Jama’a na Ofishin Jakadancin Amurka a
Najeriya, Russel Brooks ya kasance baqon shirin Rediyon Jami’ar
Legas 103.1 FM a ranar Litinin, 25 ga Fabrairu, al’amarin da ya
kasance wani yanki na bikin tunawa da tarihin baqar fata da
ofishin jakadancin Amurka a Legas ya shirya a shekarar nan ta
2019. Shirin na makonni biyu an shirya shi ne da haxin gwiwar
Jami’ar Legas da ta yi bikin watan tarihin baqar fata. A hirar
da aka yi da shi, PAO Brooks ya jaddada muhimmancin watan
tarihin baqar fata, tare da nunin cewa, “mutane na buqatar su
san ximbin al’amura game da gudunmuwar mutanen ’yan asalin
Afirka wajen bunqasa ci gaban zamani.
PAO Russell Brooks yayin da ake hira da shi a tashar rediyon UNILAG FM, inda
aka tattauna al’amuran da aka gudanar a bikin watan tarihin baqar fata
4 ga Maris | Jami’ar Legas
Taron Tattaunawa
Cibiyar nazarin ’yan Afirka da waxanda ke zaune
a qasashen waje da ke Jami’ar Legas sun ci gaba da
shirinsu na tarihin baqar fata har zuwa cikin Maris,
tare da wani shirin mai qayatarwa na tuna tarihin
mata mai taken aqidar baqaqen fata mata: haqiqani
ko hasashe. Taken darasin ya xauki hankali a wajen
tattaunawar da ta gudana a gaban dandazon masu
qwazon da suka bayar da muhimmiyar gudunmuwa
kan matsayin matan Afirka a cikin al’ummominsu da
ire-iren qalubalen da suke fuskanta. Wanda ya wakilci
Kwansula (Babban jami’in ofishin jakadanci), PAO
Brooks ya bijiro da kwatankwacin al’amuran da ake ta
muhawara kan su wannan zamanin a qasar Amurka.
Daga Hagu zuwa Dama masu tattaunawa, Dokta Irene Osemeka, Dokta Franca Attoh,
Dokta P. A Akin-Otiko, Farfesa Osita Ezenwanebe lokacin ganawar
28 ga Fabrairu | Ofishin Jakadancin Amurka, Abuja
Tattaunawar Haxakar Mutane
Ranar 28 ga Fabrairu, Ofishin Jakadancin Amurka
a Abuja ya yi bikin watan tarihin baqar fata, tare da
gudanar da tattaunawar haxakar mutane (daban-daban)
mai taken “Cike givin da ke tsakanin ‘yan Afirka da
‘yan Afirkan da ke qasashen waje.” Misis Tanya Hill
(Ofishin Jakadancin Amurka) da Farfesa Abubakar Aliyu
Liman da Dokta Rashidah Liman (Jami’ar ABU, Zariya)
da Farfesa Mabel Evwierhoma (Jami’ar Abuja), sun
tattauna kan taken darasin taron, wanda ya fito da irin
sadaukarwa da gudunmuwar da ‘yan Afirka suka bayar.
8 ga Maris | Ofishin Kwansula-Janar na Amurka,
Legas
Gasar Amsa Tambayoyi ga Xalibai
Don tunawa da zagayowar watan tarihin mata,
Shirin baje-kolin ilimi na EducationUSA a jihohin
Legas da Ogun ya shirya gasar amsa tambayoyi a
tsakanin makarantun sakandare huxu. Muqaddashin
Kwansula-Janar na Ofishin Jakadancin Amurka,
Alice Seddon ne ya qaddamar da buxe taron, inda
ya gabatar da jawabin buxe taro, tare da nuna irin
matan da suka nuna qwazo a fafutikar samar wa
al’uma mafita (daga matsalolin rayuwa), kuma sun
yi kyakkyawan tasirin inganta duniya. Makarantun
da suka halarta sun haxa da: Corolla Secondary
da School Agbara da Greenspring School Lekki da
Meadow Hall Lekki da Dowen College Lekki.
Contributors:
Grace Lamon,
Bella Ndubuisi,
16
CROSSROADS
| April/May
2019 Chibuike Ohieri, Malate-Ann Atajiri, Olaoluwa Aworinde
Misisi Tanya
Hill ke nuni kan
wani al’amari
yayin da
sauran masu
tattaunawa kan
al’amura ke lura
Muqaddashin
Kwansula-Janar,
Alice Seddon ya
yi hoto tare da
xaliban da suka
hakarci gasar amsa
tambayoyi