Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta jagoranci gudanar
da binciken ne qarqashin Ma’aikatar Lafiya
ta Tarayya da Hukumar Yaqi da Cuta mai
karya garkuwar jiki ta qasa ‘NACA’, tare da
tallafin kuxi daga Gwamnatin Amurka a
qarqashin shirin xaukin gaugawar karya
lagon cuta mai karya garkuwar jiki na
shugaban qasar Amurka, wato ‘PEPFAR.
Shawarar qwararru daga Cibiyar shawo kan
cututtuka da bayar da kariya ta Amurka
‘CDC’ ta yi matuqar tallafawa a tsawon
lokacin da alka xauka ana gudanar da
binciken.
Ranar Alhamis, 14 ga Maris, 2019, a
wani qayataccen bikin ilimantarwa
da aka gudanar, Mai girma Shugaban
tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari,
a hukumance ya gabatar da sakamakon
binciken, al’amarin da ya share fagen
baza sakamakon manuniyar binciken
NAIIS. Shugaban qasa na cikin zaquwa
lokacin da yake murnar jin labarin cewa
Najeriya na da qarancin waxanda suka
kamu da cutar qanjamau fiye da yadda
aka yi qiyasi a da. Sannan ya yi amfani da
damar wajen qaddamar da sabon nazarin
qasa na bin kadin tsare-tsaren tarairayar
cutar qanjamau/mai karya garkuwar jiki
a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021,
al’amarin da ke nuni da matakin da qasar
ta xauka kan annobar. Saboda matakin
da qasar ta xauka game da yaxuwar cutar
qanjamau, shi ne, kashi 14 cikin 100, kuma
shi ne sahihi fiye da qiyasin da aka yi a
baya, domin an xora shi a mizanin faxaxar
al’amura da dabarun bin kadin al’amura d
aaka faxaxa su.
Da yake sharhi kan sakamakon binciken,
Babban Jami’in Difulomasiyar ofishin
Jakadancin Amurka, David J. Young cewa ya
yi, Manuniyar binciken illar cutar qanjamau/
mai karya garkuwar jiki a Najeriya ta NAIIS
ta doka kyakkyawan misali kan abin da za
a iya cimmawa in an haxa qarfi an yi aiki
tare.” Sannan ya ce: “Gwamnatin Amurka
na sa ran ganin Gwamnatin Najeriya
ta qara qaimin mallaka da zuba kuxi
wajen tarairayar xaukar mataki kan cutar
qanjamau don tabbatar da xorewar ayyuka.”
Jami’in difulomasiyar ya yi sharhi kan
jajircewa mai ban mamaki da ma’aikatan
binciken suka nuna a fagen aikin, inda suka
kutsa kai har cikin surquqin gavar ruwa da
ke yankin Kudu maso Kudu da tsaunukan da
ke Arewa ta tsakiya, yayin da suka yi juriyar
qurar da ke tashi a tundurqin busasshiyar
qasar yankin Arewa maso Gabas, suka
fantsama cikin koguna ko ruquqin haqqi
da ke yankin Kudu maso Yamma da Kudu
maso Gabas, ko ma tafiyar da suka yi zuwa
sassa masu nisa na Arewa maso Yamma; sai
ya ce:”Sadaukarwar xaixaiku ta tabbata cikin
tsawon sa’o’i ana aiki da manufar inganta
lafiyar ’yan Najeriya. Jami’an binciken sun
yi tafiya a tituna masu wuyar sha’ani, sun
yi barci a wuraren da ke tattare da ximbin
qalubale, inda suka ci karo da nau’ukan
yanayin da ke barazana ga rayuwa, duk
saboda qoqarin ganin Gwamnatin Najeriya
ta samu managartan bayanai, waxanda za a
iya amfani da su don samun nasarar shawo
kan annobar cutar qanjamau/mai karya
garkuwar jiki a Najeriya.
A bayanansa, Daraktan Cibiyar shawo kan
cututtuka ta CDC a Najeriya, Dokta Mahesh
Swaminathan cewa ya yi, “Manuniyar
bincike ta NAIIS ta samar wa Najeriya da
abokan haxin gwiwarta cikakkun bayanai
masu sahihanci, da suka haxa da yaxuwar
cutar qanjamau da maganin karya lagon
qarfin cutar, tare da tasirin hana yaxuwar
cuta a tsakanin uwa da xa/’ya.” Kuma
ya ce. “Cibiyar CDC tana alfahari da
haxin gwiwarta da Gwmanatin Najeriya
da sauransu don kammala binciken.
Sakamakon da aka gabatar yana bayar da
qarin haske, kuma yana da matuqar qarfafa
gwiwa, tare da sa’ido da tantance bayanan
da aka tattara, waxanda za su taimaka wa
Gwamnatin Najeriya ta qara qaimin yaqi
da cutar qanjamau/mai karya garkuwar
jiki, ta yadda za a samu nasarar shawo kan
annobar.”
Tun cikin shekara 2004, Gwmanatin
Amurka, ta kafar shirin xaukin gaugawa
na shugaban Amurka don karya lagon cuta
mai karya garkuwar jiki na PEPFAR, ya
zuba kuxin da suka kai Dala biliyan biyar
don tallafa wa aikin shawo kan annobar
qanjamau a Najeriya, al’amarin da ya haxa
da Dalar Amurka miliyan 70 don tallafa
wa ayyukan binciken manuniyar illar
cutar qanjamau/mai karya garkuwar jiki a
Najeriya na “NAIIS”.
Muhimman mutanen da suka taru sun haxa da Dokta Sani Aliyu, Daraktan NACA (na 2 daga hagu) da Muhammadu Buhari, Shugaban qasar Tarayyar Najeriya (na 4 daga hagu) da Dokta Isaac Adewole, Ministan
Lafiya (a tsakiya) da David Young, Babban Jami’in Difulomasiyar Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya (can nesa daga dama) sun taru don xaukar hoto lokacin da aka gabatar da sakamakon binciken NAIIS
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
15