Magama MAGAMA Yuni/Juli 2019 | Page 14

LAFIYA ...YUNQURIN A KAWO QARSHEN ANNOBAR QANJAMAU A NAJERIYA likitanci in ana son samun nasarar warware ruxanin da ke tattare da rashin lafiya, muna buqatar tantancewa managarciya; muna buqatar sanin tarihin majinyaci, ta yadda za mu fahimci yadda asalin cutar ta faru da bunqasarta, al’amarin da zai zamo manuniyar halin da ake ciki a yanzu, sannan a cimma matsaya kan magungunan da suka fi dacewa ko dabarar da za a bi wajen warkar da cutar. A mafi yawan al’amura irin waxannan, kyakkyawar dabarar tantance cuta, ita ke bayar da hasken yadda za a maganceta. Daga Halilu Usman 14 MAGAMA | Mayu/Yuni 2019 Manuniyar nazarin binciken cutar qanjamau/mai karya garkuwar jiki a Najeriya (NAIIS), an vullo da ita ne don samar da sahihiyar hanyar tantance annobar cutar qanjamau/mai karya garkuwar jiki a Najeriya, ta mahangar kula da lafiyar al’umma. Don aiwatar da wannan aiki a qasar da take da yawan al’umma da ya kai miliyan 190, waxanda suka bazu a xaukacin wurare masu nisa da surquqin wurare masu wuyar sha’ani, akwai buqatar fiye da xaixaikun mutane ’yan kaxan don tantance sahihancin kamuwa da cuta. Manuniyar bincike ta ‘NAIIS’ ita ce babbar hanyar binbciken ximbin al’umma kan cutar qanjamau/mai karya garkuwar jiki in an bi gidajen iyalai a duniya, ta yadda akan tattaro xaixaikun mutane a wuri guda, inda manufar kawai ita ce, ta samar wa Najeriya cikakken bayani game da annobar qanjamau/mai karya garkuwar jiki. Binciken ya kai kimanin 250,000 na mutanen da aka bibiyi kadin lamarinsu, waxanda aka same su kusan a gidajen iyalai 100,000, aka kuma tattara bayanansu a kan kari. An gudanar da aikin ne ta hanyar baje taswirar sassan qasa da kayan aiki da sufuri da tunkarar qalubalen tsaro, al’amarin da a halin yanzu yake faruwa a Najeriya. Manuniyar binciken NAIIS an tsarata ne ta bibiyi gidajen iyalai don tantance yaxuwar cutar qanjamau da samun haske kan al’amuran da suka shafi lafiya. Bayanan da aka tattara an samu nasarar kammala su tare da tattare su a cikin tsarin lokaci, Yulin 2018 zuwa Disambar 2018, don tabbatar da ana da bayanan a qasa, waxanda za a yi amfani da su wajen tsare-tsaren magance cutar qanjamau da dabarun hana kamuwa da ita a shekarar nan ta 2019. Bayan da aka tattara an samar da su ne ta hanyar bibiyar ahalin iyalai da shekarunsu suka kama daga 0 zuwa 64 da kuma bayar da shawarar sirri wajen tarairayar cutar qanjamau, tare da gwaji, su aka gabatar wa mutanen da aka gudanar da binciken a kansu. Xaukacin waxanda aka gudanar da binciken a kansu, waxanda aka gano sun kamu da cutar qanjamau, an haxa su da wata cibiyar kula da lafiya, don su samu magungunan cutar qanjamau na ARV kyauta. Bayanan da manuniyar bincike ta NAIIS ta tattara sun haxa da matakin qasa da yanki da jiha xauke da bayanai kan ayyukan shawo kan cutar qanjamau a