SHIRIN MUSAYA
MANYAN ZAVUKAN NAJERIYA:
Gudunmuwar YALI
Daga Diran Adegoke
Z
avukan Najeriya da suka gabata
an samu ximbin matasan da suka
shiga aka dama da su; matasan sun
yunquro don kama ragamar kujerun mulki
kan teburan cimma matsayar al’amura
a Najeriya. Matasa 400 sun yi amfani da
wannan damar kan doron dokar da aka yi ta
rage shekarun takarar muqaman siyasa wato
“Not Too Young to Run” dokar da ta bayar
da damar yin takarar muqaman Gwamnati
a matakai daban-daban a zavukan da aka
kammala a Najeriya.
Shirin liqon alaqar ‘YALI-Network’ ya yi
matuqar tasiri a tsakanin matasan Najeriya
da ’ya’yan qungiyar sa-kai waxanda suka yi
dandazon tallafa wa tsarin gudanar da zave
ta kafar fafutikar liqon alaqar YALI Network
NaijaVotes. Fafutikar zave ta NaijaVotes
an tsara ta ne a doron manufar Amurka ta
wucin gadi da dogon zango da ke da alaqa
da zaven Najeriya, wanda ke da manufofi
uku:
• Qarin shigowar masu kaxa quri’a da
fahimtar yadda ake yin zave cikin qimar
daraja (ba sayar da quri’a ba) –
• Bayar da qwarin gwiwar yin gaskiya
da tabbatar da nagartattun bayanan da ake
bazawa (ba labaran qarya ba) -
• Nusar da al’ummomi su kauce wa tashin
hankali da kalaman vatancin nuna qiyayya
Wasu daga jerin ayyukan da aka gudanar
sun haxa da kutsawa yankunan karkara
da tallata manufa a kan tituna da isar da
saqonniinn waqe-waqe da hotunan bidiyo
da aka riqa yaxawa ta kafar rediyo da
shafukan sada zumunta na intanet, tare
da tattaunawar xakin taron gari da tafka
muhawarar ’yan takara da saqonnin manyan
alluna tare da kai ziyara ga qungiyoyin
addinai da jami’o’i da sarakunan gargajiya.
Liqon alaqar YALI da ke horar da matasa
yadda ake jagorancin al’umma ya yi aikin
haxin gwiwa da shirin yaxa manufar hana
faxace-faxace a yi zave ba tare da faxa ba
na #VoteNotFight program ga Gidauniyar
Youngstar da Hukumar Raya ci gaban
qasashe ta Amurka ‘USAID’ ta xauki
nauyinsa don tabbatar da an yaxa manufar
zaman lafiya a kowace xaya daga cikin jihohi
36 da ke Najeriya a shirin Aikin Ranar qasa
na ‘NDA’
Don tallafa wa wannan yunqurin ofishin
jakadancin ya shirya shirin gabatar da
jawabi ta kafar sadarwar intanet na ’ya’yan
qungiyar liqon alaqar YALI 100 da ke
cibiyoyin Amurka biyar (5 American
corners). ’Yan majalisar Amurka biyu da
suka yi murabus, waxanda suka shiga shirin
Xan qunqiyar YALI Network lokacin da yake ganawa da al’umma a Kasuwar Dutse da ke Abuja
12
MAGAMA | Mayu/Yuni 2019
sun yi magana kan manufar Amurka na
tabbatar da managarcin zave da yin zave
nagari da bin kadin sauke nauyin al’umma
da tabbatar da gaskiya qeqe-da-qeqe da
kyautata dangantaka tsakanin ’yan majalisa
da mazavu ta wajen sauke nauyin da ya
rataya a kansu.
Faxakarwar kaxa quri’a mai taken
‘NaijaVotes’ ta xauki hankali Cibiyar
Nazarin Dimokuraxiyya da Raya qasa a
Najeriya, wadda ta riqa yaxa saqonnin
NaijaVotes da sauran bayanan da ke qunshe
a saqonninta na faxakarwa kan harkokin
zave, sannan ta samar da ’yan qungiyar liqon
alaqar YALI waxanda suka yi aikin sa-kai
na sa’ido kan harkokin gudanar da zave a
jihohi 21.
Yayin da aka fafata takarar zave tare da
samun tashe-tashen hankula, qwararrun
masana sun ce al’amuran ba su da yawa,
savanin yadda aka yi hasashen aukuwarsu
a da, inda ximbin matasa suka qi yarda a
yi amfani da su wajen tayar da rikici, tare
da faxakarwa kan labaran qarya, ta yadda
bayan an ankarar da muninsu, sai aka yi
qoqarin shawo kan bazuwarsu. An samu
ximbin waxanda suka yi rajistar yin zave,
amma in an kwatantata da yawan waxanda
suka kaxa quri’unsu sai a ga cewa sun yi
qaranci.
Allon isar da saqon kaxa quri’ar zave na NaijaVotes a Warri, Jihar Dalta