Magama MAGAMA Yuni/Juli 2019 | Page 11

O B abu abin da ke da qimar martaba fiye da rayuwar xan Adam. Duk sa’adda aka yi rashin wani lamarin kan kasance wata mumunar musifa – ko da mutumin manomi ne ko makiyayi ko Musulmi ko Kirista, xan qabilar Berom ne ko Bafullatani. A shekaru biyu da suka gabata na ziyarci Filato, haka ma jihohin Zamfara da Kaduna da Sakkwato da Edo da Neja. A kowane xaya daga waxannan wurare na ga illar mummunan tashin hankali da ya cutar da ximbin mutanen karkara da ke zaune a waxannan sassa na Najeriya. An hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, an tarwatsa al’umma, mutane sun waste sun bar gidajensu, yayin da iyalai ko zuri’a ke taruwa su yi makokin rashin ahalinsu. Daidai wancan lokacin na ga babbar musifa, na ga kuma mutanen da suka yi tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya (a tsakanin al’umma). Na ga waxanda suka sadaukar da rayuwarsu, ta hanyar tunkarar haxurra don kare wasu (da ke zaune) a cikin al’ummarsu. Shi ya sa zan gabatar muku da wani xan Najeriya, dattijo mai shekara 83, Limamin qauyen Nghar da ke cikin Qaramar Hukumar Barikin- Ladi, wato Imam Abdullahi Abubakar. Zan bayyana muku labarin lamarin ban mamaki game da wannan limami, kan abin da ya yi wajen ceton rayuka, saboda ina jin cewa mutane da dama a qasar nan ba su san wannan mutumin mai matuqar ban-mamaki ba. Kimanin watanni tara da suka wuce wasu ‘yan bindiga sun kai farmakin mamaya a qauyen Inyar. Sun kunno kai ne da sassafe a kan Babura xauke da bindigogi samfurin AK47 da addunan sara. Da waxannan makaman sara suka halaka mutane. Sun qona gidaje. Qauyen da al’ummar cikinsa ba su fi dubu ba, an yi asarar rayuka 84. Mata da maza da qananan yara da aka yi wa kisan gilla saboda qiyayya da mummunan manufar matasan da ke da mummunan tunani saboda rashin tarbiyyar da ta xamfaru a irin fahimtar da suka yi wa wannan duniyar. Amma daidai lokacin aukuwar wannan mummunar musifa, Imam Abdullahi Abubakar da mataimakansa duk Fulani sun yi wasu muhimman abubuwan ban mamaki. Lokacin da maharan suka fara harbe-harbe da sare-sare, xaruruwan mutane suka fara gudun tsira da rayuwarsu. Mutane xari biyu da sittin suka gudu zuwa masallaci. Kodayake Babban Jami’in Difulomasiya, David Young, tare da Ishaku Abdullahi, xan Imam Abdullahi da Malam Abdullahi Umar, Na’ibin Limamin masallacin qauyen Nghar suka yi hoto tare da Imam Abubakar mafi yawansu Kiristoci ne da ’yan qabilar Berom, Liman da Na’ibinsa suka tara su a cikin masallacin sai suka kulle qofa. Imam Abdullahi ya kai wasu mutanen gidansa da ke kusa da wurin. Sai kuma limamin da na’ibinsa suka koma suka ja daga a waje. Daidai lokacin da maharan suka iso daf da qofar shiga wurin, sai liman da na’ibinsa suka ce “Ba za ku shiga ba, domin sai dai in kun kashe mu za ku iya kutsa kai ciki.” Daga nan sai Imam Abdullahi ya tsugunna da gwiwoyinsa a qasa yana roqon ‘yan bindigar su juya (su tafi abin su), ka da su kassara rayuwar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, kuma suna cikin al’ummarsa, su abokansa ne da ya sani tsawon shekaru. Kiristoci ne da suke yin bikin Kirisimeti tare, tamkar yadda suke yin bikin Sallah tare da shi. Saboda wannan abokantaka tasu da jajircewasu da nuna ‘yan uwantakarsu a tsakanin mazansu da matansu, sai ya sadaukar da rayuwarsa, inda fiye da mutane 300 suka tsira, domin ‘yan bindigar sun juya. Ni na ziyarci qasashe fiye da 80, ba na jin na tava haxuwa da mutum irin Liman Abdullahi. Waxanda ke qoqarin tabbatar da zaman lafiya, ba wai rukuni guda ba ne ko wasu daban. Ba kawai Musulmi ba ne, ba Kirista ba ne, ba wai sun fito daga rukuni guda ba ne ko wata jiha. Sun kasance xaixaikun mutanen da suka jajirce kan kyakkyawan al’amari da yaqin fatattakar mugun abu. Liman Abdullahi ya zama zakaran gwajin dafi (mai zaburarwa ga aikata kyakkyawan aiki) tare da qalubalantar xaukacinmu. Shin ko muna iya sadaukar da rayuwarmu don zaman lafiya da bayar da kariya ga mutanen da suka fito daga wasu al’ummomi (daban da namu)? Yi tunani kan abin da wannan lamarin ke nuni ga qasar nan da duniya baki xaya. Savatta-juyartan tashe-tashen hankula da hare-hare da xaukar fansa da taho-mu-gamar xaukar fansa suna kassara ximbin rayuka, na xaukacin Kiristoci da Musulmin da ake kashewa. Yin aiki don tabbatar da zaman lafiya na ceto rayuka, kuma shi ne abu mafi martabar daraja a wannan duniya. Wannan qasa mai matuqar son addini ce. Qasar imani inda ’ya’yan Ibrahima, ’yan uwa maza da mata ke bin manyan addinan duniya biyu – Kiristanci da Musulunci – suna masu miqa wuya wajen ibada da addu’a a kowane mako, kowace rana. Kuma sun miqa wuyansu wajen aikin tabbatar da zaman lafiya da nuna qauna (a junansu) da tabbatar da adalci. Sai dai a wasu lokutan mukan ga mutanen da ke xaukar mataki bisa irin imaninsu. A wajena wannan tunatarwa ce, cewa mafi muhimmancin al’amari abin da za a mu iya yi shi ne, mu cusa wa zukatanmu kyawawan tsarkakan manufofi. Fatana dai a ce xaukacinmu za mu iya sarayarwa mu sadaukar da rayuwa tamkar yadda waxannan managartan limamai da ximbin wasu mutanen da suka yi aiki tuquru a kai- a kai don tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato. Na sha jin irin waxannan labarai daban- daban na masu fafutikar zaman lafiya, shi ya sa fatana dai kowanenmu a ce mun yi iya yinmu (bakin qoqarinmu) don tabbatar da zaman lafiya, ta yadda za mu cimma matsayar kawo qarshen tashe-tashen hankula. MAGAMA | Mayu/Yuni 2019 11