Sake salo da
shiryawa
DAN JARIDA
jarida su kasance masu qulla alaqa tsakanin
al’ummar qasa da shugabanninsu.
daga Sani Mohammed
Bitar kwana biyu kan hada-
hadar sadarwar intanet
don kaifafa basirar ‘yan
jarida kan rahoton zave.
O
fishin Jakadancin Amurka da ke
Abuja ya shirya bitar kwanaki biyu
kan gudanar da ayyukan zahiri
da na shafukan intanet ga wakilan kafafen
yaxa labarai da ke xauko labaran siyasa,
mahalarta bitar sun fito daga kafafen yaxa
labarai a Abuja, inda suka yi nazarin jam’iyo
a cibiyoyin Amurka da ke Ibadan da Kalaba
da Kano da Bauchi, a tsakanin ranakun 13
ga Nuwamba zuwa 14 na shekarar 2018.
Horon da aka ba su manufa ce ta Ofishin
Jakadancin Amurka na tallafa wa Najeriya
wajen gudanar da zaven shekara ta 2019.
An tsara gudanar da manyan zavukan
Najeriya a tsakanin 16 ga Fabrairu zuwa 2
ga Maris xin shekarar 2019. Gwamnatin
Amurka ta sha nanatawa cewa tsarin
gudanarwa take tallafawa ba wai wani
xan takara ba, sai dai abin lura a nan shin
Amurka na tallafa wa tsarin gudanar da
zaven ne kamar yadda ta yi iqrari, a cewar
Jakada W. Stuart Symington lokacin bitar.
Babban Editan jaridar intanet, wanda ya
samu lashe kyauta, Musikilu Mojeed shi ya
jagoranci bitar aiki a bayyane, yayin da wani
magabatar da jawabi a taruka xan Amurka,
Farfesa Gary Kebbel, Farfesa a fannin
nazarin aikin jarida a Jami’ar Nebraska-
Lincol, da Manajan Editoci Aliyu Mustapha
da abokin aikinsa Peter da Clottey suka
gabatar da shirin talabijin na “gaba-dagaba”
da shirin Nighline Africa” na rediyo waxanda
aka gabatar a wajen bita ta kafar intanet a
taron na kwanaki biyu.
Farfesa Idachaba, Darakta sa-ido kan
harkokin yaxa labarai a Hukumar Watsa
Labarai ta qasa (NBC) da Lauya Festus
Okoye da Kwamishinan qasa, kuma
shugaban sashen yaxa labaran Hukumar
zave ta INEC suka gabatar da jawabai, daya
qara wayar da kan ‘yan jarida suka qara ilimi
kan dokoki da qa’idojin kawo rahoton zave.
Jakada Symington yace duniya ta zuba
wa Najeriya ido don ganin ta gudanar da
zave mai inganci da adalci cikin kwanciyar
hankali a shekarar 2019, inda ya buqaci ‘yan
Musikilu Mojeed, Babban Editan Jaridar Intanet ta Premium Times ke jagorancin taron bita
“A tsarin dimokuraxiyya, inda ake da ‘yanci
a qasar da keda al’umma, dole ne a samu
hanyoyi biyu na isar da saqo kuma kafafen
yaxa labarai su ne mavuvvugar bayanan
dake danganta mutane da shugabanninsu,”
inji Jakada Symington.
Horon bitar na kwanaki biyu, ya haxa da
tattaunawar wani lokaci da aka ware, inda
mahalarta suka samu damar nazarin bin
kadin al’amuran da suka wakana a cikin
rahotannin qalubalen da aka fuskanta a
zavukkan da suka gabata, sannan suka koyi
managartan dabarun da suka dace daga
masu bayar da horon tsakanin Washington
da Abuja.
Xaukacin waxanda suka bayar da horon
bitar da manyan baqi da suka gabatar da
jawabi, sun jadadda buqatar da ake da ita
a wajen ‘yan jarida don taimakawa wajen
wayar da kan al’ummar qasa kan tsarin
gudanar da zave, sannan su tunkari ‘yan
siyasa kan matsalolin da ake fuskanta. Kuma
sun shawarci ‘yan jarida kan bayyana ra’ayin
masu kaxa quri’a a rahotanninsu, su kauce
wa son rai, ko kare muradun wani vangare
ko cusa wani ra’ayi (daban), don yin hakan
kassara nagartattun tsare-tsaren kariya
lokacin zave, tare da dabarun tantance
bayanan gaskiya.
Jerin mahalartan bitar
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
9