Magama Disamba 2018/Janairu 2019 | Page 10

USAID TARAIRAYAR MUTANEN NAJERIYA daga Zack Taylor Amurka na hanqoron ganin ‘Mutanen Najeriya’ sun samu nasara a zave mai qaratowa. USAID na tallafawa don tabbatar da sahihancin quri’un da za a kaxa a cikin lumana 10 D a aka tuntuvi Jakadan Amurka a Najeriya, W. Stuart Symington kan ko wanene gwamnatin Amurka ke son ya yi nasarar lashe zave a zaven shugaban qasa da ke qaratowa, a koda yaushe amsar Jakada W. Stuart Symington ita ce Amurka na hanqoron ganin “Mutanen Najeriya” suka yi nasara a zaven Shugaban qasa da ke qaratowa. Tamkar zavukan 2015 da na 2011 da suka gabace shi, Ofishin Jakadancin Amurka ya tallafa wa tsarin gudanarwa (yin zave) ne ba xan takara ba a zavukan da za a fafata masu qaratowa na shugabancin Najeriya da gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisar dokoki a shekarar 2019 Tamkar zavukan da suka gabata, ofishin jakadancin Amurka na fafutikar tabbatar da tsaftar zave da yin gaskiya qeqe-da-qeqe, uwa-uba ma shi ne a gudanar da zaven cikin lumana. Don cimma manufar, Hukumar Amurka d ake tallafa wa Ci gaban qasashen duniya ta USAID ta bayar da gudunmuwa ga Hukumar zave ta qasa (INEC) da qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma da jam’iyyun siyasa don inganta ayyukan ilimantar da masu kaxa quri’u da bunqasa ci gaban jam’iyya da tallafa wa aikin ‘yan qasashen waje masu sa-ido don inganta zaven, ta yadda za shigo da kowa-da-kowa zaven ya MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019 gudana babu tashin hankali. Tun a shekarar 2014, Hukumar USAID ta ware Dala miliyan 58 da dubu 200, tare da tallafin kuxin daga Hukumar Raya ci gaban qasashe ta Birtaniya DfID, wadda ta samar da Dala miliyan 18 da dubu 600 don taimaka wa Hukumar zave ta qasa, wajen aiwatar da sauye-sauye da gyare- gyare don tabbatar da ingancin da sahihancin zavuka, sannan ta taimaka wa qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma, waxanda suka himmatu da ayyukan kula da gangamin faxakarwa ga masu kaxa quri’a, ta yarda za a riqa qarfafa gwiwar rukunin waxanda ake tauye haqqinsu, musamman mata da nakasassu, tare da kawar da duk wata tashintashina da ka iya haifar da tashin hankali. USAID ta tallafawa harkokin tafiyar da ragamar mulkin Hukumar zave na gudanar da zave, da tsara dabarun yaxa manufofi na jam’iyyu, da wayar da kan masu yin zave kan haqqoqinsu da gudunmuwar da za su bayar wajen kafuwar tafarkin dimokuraxiyya a xaukacin matsayinsu na masu yin zave da yin takarar muqamai. “Zaman lafiya da sahihancin zavuka su ne jiga- jigan al’amuran da za su tabbatar da bunqasar ci gaban Najeriya,” a cewar Daraktan Ofishin Jakadancin Amurka, Stephen M. Haykin.