‘Tallafinmu na Zavuka na taimakawa
wajen share fage ga ‘yan Najeriya su zavi
shugabannin da za su yi jagoranci bisa
tafarkin dimokuraxiyya, ta yadda za su
kyautata walwala da jin daxin al’ummar
qasa. Bisa la’akari da wannan, tallafinmu na
tabbatar da sahihanci da adalcin zave na da
muhimmanci tamkar kowane aiki da muke
yi.”
Gyara fasalin zave da Hukumar INEC
Dalilan da ke sanya al’ummar Najeriya
su iya amincewa da tsare-tsaren ayyukan
Hukumar Zave da sakamakon zave, dole ne
a kawar da duk wani shakku. Don cimma
wannan manufa, Hukumar USAID ta
horar da jami’an Hukumar Zave ta INEC
kan tsarin tafiyar da hakokin mulki da
hadahadar ayyukan zave, tare da bayar da
horo kan fannonin da suka shafi tsarin tsaro
da dabarun warware taqaddamar rikici, tare
da dabarun shigowa da xaukacin masu kaxa
quri’a a tsare-tsaren gudanarwarta.
Hukumar USAID na taimaka wa Hukumar
zave ta INEC wajen qulla alaqar ayyuka
da tabbatar da nagarta da ingancin zave,
wajen tarairayar ayyuka, kan al’amuran da
suka haxa da tallafa wa cibiyoyin sa-ido
wajen rarraba kayan aiki da tattara quri’un
da aka kaxa, da tsara quri’un, tare da samar
da kayan ilimantar da masu kaxa quri’a;
tabbatar da shirin kotunan shari’a wajen
karvar qara/qorafe-qorafe kan harkokin
zave; bayar da horo kan samar da dabarun
warware taqaddamar rikicin zave; sannan a
wayar da kai kan yawan kuxi da ya kamata a
kashe wajen yaqin neman zave.
Qarfafa qungiyoyin fafutikar haqqoqin
al’umma
Hukumar USAID na inganta ayyukan
qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma
kan yadda za su sa-ido wajen gudanar da
zave, inda ta horar sama da mutane 3000
masu aikin sa-ido don su fitar da jaddawalin
kaxa quri’u bisa tsarin ‘PVT’ ko ‘qidayar
hanzari,’ wata hanyar mai cin gashin kanta
da ake amfani da ita wajen tantance inganci
sakamako a ranar zave. Sannan akwai
dabarar ankararwa kan yiwuwar tashin
hankali, ta yadda akan fitar da nuniyar
alamun da ka iya haifar da rikici.
“Xaukacin ayyukan na da manufar bunqasa
qwarerwar rukunin ‘yan qasa, ta yadda za
su iya shiga a dama dasu a harkokin mulkin
qasarsu,” a cewar Aubrey McCutcheon,
babban Daraktan Cibiyar Nazarin Harkokin
Dimokuraxiyya ta qasa, kuma tsohon abokin
haxin gwiwar USAID kan harkokin zave.
“yayin da xaukar xawainiya kuxi ke zuwa
daga qasar waje, horon ya qarfafa qungiyoyin
cikin gida da ke fafutikar haqqoqin al’umma,
waxanda suka himmatu da aikin gangamin
wayar da kan ‘yan Najeriya don tabbatar
da sahihancin zave ta hanyar kauce wa
kurakurai.
A cewar McCutcheon jadaddawalin
sakamakon zave na ‘PVT’ na bai wa
al’ummar qasa da qungiyoyin da ba na
gwamnati ba damar tantance sahihancin
sakamakon zaven da Hukumar zave ta INEC
ta fitar a qashin kansu, inda sukan tabbatar
da ingancinsa ta hanyar amfani da samfurin
qididdigar quri’un da aka kada a rumfunan
zaven kowace qaramar hukuma da ke faxin
qasar nan.
Kuma ana cure bayanai bisa managartan
dabarun sa-ido kan kowane al’amari da aka
gudanar wajen zave har zuwa kan kaxa quri’u
da qidaya su, inda daga bisani aka samar da
rahoton sakamakon da ya yi ‘hannun riga ko
sha bamban’, bisa la’akari da kura-kuran da
Masu aikin sa-kai na shigar da alqaluman jaddawalin PVT a Zaven gwamna da aka
gudanar a Jihar Osun cikin satumbar 2018
suka shafi barazana ko firgici da sayen quri’a,
tamkar yadda ta faru qarara a zaven Satumba
da aka gudanar a Jihar Osun. Muhimman
al’amura da akan lura da su kafin gudanar da
zave, ankararwar tashin farko kan alamun
al’amura da ka iyar haifar da rikici, a bayar da
rahotanni ga qungiyoyin fafutikar haqqqoqin
al’umma da hukumomin tsaro don kawar da
duk wata tsashintashinta kafin ta munana.
Zaburar da matasa
Hukumar USAID ta bayar da muhimmiyar
gudunmuwa wajen tarairayar shugabannin
siyasa, ta hanyar qarfafa gwiwar qungiyoyin
matasa su juya akalar harkokin siyasar qasa,
domin a cewar Obinna Udenwa, mai shekaru
30, wanda ya taimaka wa ayyukan Hukumar
USAID na tallafa wa matasa a qarqashin
gidauniyar Youngstar, kuma a halin yanzu
shi xan takarar muqamin siyasa ne a Jihar
Ebonyi.
A cikin tsare-tsaren ne aka haifar da
mahangar daqile qarancin shekarun matasa
na yi takarar muqamai, al’amarin daya bijiro
da buqatar rage yawan shekarun yin takarar
muqamin siyasa, har ya samu rattaba hannun
amincewar Shugaba Muhammadu Buhari a
Mayun 2018.
“Sai dai wannan bai isa ba,” a cewar Udenwa
da yake tsokacin kan sabuwar dokar.
“tsofaffin shugabannin Najeriya ba su da
shirin horar da matasan da za su maye
gurbinsu a matsayin shugabanni. Dole ne
matasa su tunkari wannan qalubalen.”
Tsawon tarihi, a cewar McCutcheon matasa
sun kasance ‘yan baranda a zavukan Najeriya
– don ‘yan siyasa kan yi hayarsu da su tayar
da rikici, inda ‘yan kuxi qalilan kan ruxe
su, har su yamutsa rumfunan zave da satar
akwatunan zave ko ma su aikata abubuwan
Daraktar Jaddawalin alqaluman zave na PVT, Cynthia Mbamalu ke bayyana wa Kwamishinan
Hukumar Zave, May Agbamuche-Mbu yadda tsarin jaddawalion alqaluman ke gudana
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
11