Magama Disamba 2018/Janairu 2019 | Page 12

Innocent ‘2baba’ Idibia tare da ’yan sa-kai a gidauniyarsa ta Youngstars Foundation, inda suka gana da Gwamnan Jihar Anambra state governor, Willie Obiano kafin gudanar da zaven Gwamna a 2017 da suka fi hakan muni. Wanzar da zaman lafiya A yunqurin shawo kan matsalolin da ake cin karo dasu, Hukumar USAID na tallafawa wajen faxakarwa don kyautata xabi’u, ta hanyar zaburar da matasa su himmatu ka’in d ana’in (a harkokin siya), tare da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a wajen gudanar da ayyuka. Tun a shekarar 2014, aka fito da shirin faxakarwa mai taken ‘Kaxa quri’a ba faxa ba ne: Zave ba yaqi ba ne, shirin da aka tsara da manufar wanzar da zaman lafiya, ta hanyar al’amuran da suka haxa da waqe- waqe da raye-rayen isar da saqon zaman lafiya, inda shahararren xan wasa a kafafen yaxa labarai Innocent mai laqabin “2Baba”. ya cashe. A matsayinsa na Jakadan wanzar da zaman lafiya, “2Baba.” Ya jagoranci jan ragamar rajistar masu kaxa quri’a, kuma ya xauki nauyin shirya faxakarwa, inda ‘yan takara suka rattaba hannu kan alqawuran tabbatar da zaman lafiya, sannan su jajirce wajen cika alqawuran da suka xaukar wa al’umma da zarar an zavesu. Bazuwar ximbin shafukan sada zumunta na intanet sun bayar da muhimmiyar gudunmuwa wajen jawo matasan Najeriya su shigo fagen siyasar qasarsu a dama da su, inda Hukumar USAID ta jajirce wajen tallafawa xaukacin ayyukan kafafen sadarwa a qarqashin alamun sadarwa masu taken #kaxaquri’a ba faxa bane - VoteNotFight #ElectionNoBeWar – Zave ba yaqi ba ne, 12 wanda aka riqa yaxawa a tashar talabijin ta qasa zuwa qananan tashoshi, don yin kira da faxakarwa kan wanzar da hada- hadar tabbatar da zaman lafiya qarqashin jagorancin 2Baba da Gidauniyarsa da ta himmatu wajen bijiro da al’amuranm da ya kamata a riqa tattaunawa akai, ta yadda za su kawar da tashin hankalin da ka iya aukuwa ranar zave. “Ayyukan 2Baba sun sauqaqa ayyukan sauran qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma,” a cewar McCutcheon. Jawo jam’iyun siyasa a dama da su Hukumar USAID na tallafa wa wajen bunqasa managartan dabarun jawo jam’iyyun siyasa a dama da su, ta hanyar qarfafa su wajen tarairayar mazavu da samar da kafar tafiya tare da gwamnati a wajen gudanar da ayyuka, inda akan taimaka wa mafi yawan jam’iyyun don zama wakilan da ke iya xaukar matakin biyan buqatun al’ummar qasa. Ba wai kawai Hukumar USAID na taimakawa wajen yin hada-hada da kowa-dakowa ba a matakin mazavu, har ma da qarfafa tsarin sadarwa a tsakanin jami’an jam’iyya da masu riqe da muqamai da ‘yan takara, har ma da masu qaramin muqami qananan ma’aikata a kowane mataki. “Munma iya yin qoqarinmu wajen qulla alaqa tsakanin al’ummar qasa da harkokin mulki don tabbatar da cewa al’ummar qasa ana damawa da su a harkokin siyasa,” a MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019 cewar Sentell Barnes, Babban Jami’in Cibiyar Nazarin qimar matsayin al’umma a kan Jagoranci ta Najeriya, wato International Republican Institute in Nigeria, wani abokin haxin gwiwar USAID wajen tallafa wa harkokin gudanar da zavuka. “Ta hanyar tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna tafiya da ‘ya‘yansu, sannan suna jawo al’ummar qasa don fahimtar matsalolin al’umma, ta yadda idan suka kama ragamar mulki, za mu tabbatar da cewa an warware waxannan matsaloli ta hanyar da ta dace.” A qarshe dai, Gwamnatin Amurka, ta hanyar ayyukan Hukumar USAID, na son taimakon Najeriya wajen bin qa’idojin dimkuraxiyya, a cewar Barnes. Kuma shirin (taimakon) ya haxar da tabbatar da sahihanci da adalci a zavuka, ta yadda jam’iyyu za su riqa gudanar da harkokinsu ba tare da katsalandan (ko tsangwama) daga jami’an gwamnati ba, sannan Hukumar Zave ta INEC ta tabbatar da cewar ta tanadi cikakkun kayan aikin gudanar da zavuka masu tsafta da inganci. “Ina da tabbacin kan qarfin ikon mutane na zaven shugabanninsu,” inji 2Baba. “Kuma ina da tabbacin cewa akwai buqatar gudanar da zavuka cikin lumana da wayewar zamani. Aikata savanin haka kuwa, zai sanya mu yi babbar asara. Sai a tuntuvemu domin qarin bayani kan tallafin hukumar USAID a Najeriya kan shafin intanet na: https://www.usaid.gov/elections-0