Da tallafin USAID, matasan Najeriya
suka tabbatar da qarancin shekaru ba
ya hana takarar muqaman jan ragamar
Shugaban qa sa ya sa hannu kan dokar rage
al’umma
yawan shekarun takarar muqaman siyasa
daga Zack Taylor
Q
udurin da ya yi shekara biyu yana kai-
kawo a majalisar qasa, tare da goyon
bayan qungiyoyin Najeriya masu
fafutikar haqqoqin al’umma don ganin an rage
yawan shekarun yin takarar muqaman siyasa
na shiga majalisa da shugabanci ya samu kaiwa
ga gaci, inda a wannan shekarar aka kawo
qarshen taqaddamar. Inda a farkon wannan
shekarar Shugaban qasa Muhammadu Buhari
ya rattaba hannun tabbatar da qudurin
“Matasa ba su da qarancin shekarun takarar
muqaman siyasa (Not Too Young to Run). wannan quduri har ya kai gaban shugaban
qasa sun zaqu a basu damar jagoranci,” a cewar
xaya daga cikin waxanda suka yi fafutikar
tabbatar da sabuwar dokar, kamar yadda ya
rubuta ba dadaxewa ba kafin qudurin ya samu
wuce a gaban majalisar qasa.
Sabuwar dokar ta rage yawan shekarun takarar
majalisun dokoki daga 30 zuwa 25, sannan na
shugaban qasa daga 40 zuwa 35, inda a karo
na farko za a yi wa Kundin tsarin mulkin 1999
gyaran fuska ko garambawul (gyare-gyaren
dokoki) don faxaxa damar shigar da matasa
takarar muqaman don jangorancin al’umma a
zavuka. horo tare da yin gangmain zavurarwa ga
jami’an yaxa manufar kawar da qarancin
shekarun matasa na yin takara a xaukacin
jihohi 36 na Najeriya, an xauki nauyin
xawainiyar “kwanakin xaukar mataki a faxin
qasa” kan al’amura, tare da isar da saqonni ta
kafofin yaxa labarai a xaukacin faxin qasar.
Hukumar Raya Ci gaban qasashen duniya ta
Amurka, wato ‘USAID’ tare da haxin gwiwar
Hukumar Raya ci gaban qasashe ta Birtaniya,
wato DFID’ sun bayar da gudunmuwa har
aka kai ga nasara, ta hanyar fafutikar bayar
da horo ga jami’an yaxa manufa a xaukacin
jihohi 36, tare da faxaxa ayyukan faxakarwa
ga al’umma.
“A matakin qarshe na tabbatar da wannan
manufa, matasan Najeriya da suka ingiza
Ta hannun abokiyar haxin gwiwar aiwatarwa,
wato Cibiyar Dimokuraxiyya ta Qasa (NDI),
tare da tallafin kuxi daga DfID da USAID,
waxanda suka taka muhimmiyar rawa, wajen
bayar da
Tushen asalin wannan fafutika dai ita ce
qungiyar bunqasa ci gaban rayuwar matasa
ta Afirka (YIAGA), wata qungiyar fafutikar
haqqoqin al’umma a Najeriya da ta jajirce
wajen tallafa wa matasa da kiran gangamin
shiga a dama da su a harkokin siyasa, don
tabbatar da gaskiya qeqeda-qeqe.
Tashin farko dai qungiyar YIAGA ta fara
tuntuvar cibiyar nazarin dimokuraxiyya ta
qasa a baya cikin shekarar 2016, in data buqaci
haxin gwiwarta wajen sabunta nazarin tsare-
tsaren harkokin matasa, sai kwatsam lamarin
ya rikixe, inda ya bunqasa har ta kai ga
fafutikar gyara a kundin tsarin mulki, ta yadda
za a jawo ximbin matasa su shiga harkokin
siyasa.
Lokacin da yaxa manufar ta qara faxaxa ta ya
zama babbar qungiyar fafutika, sai qungiyar
YIAGA ta nemi gwarazan ‘yan majalisa,
irin su xan majalisar dattijai Jonathan
Zwingina, wanda ke da ra’ayin muhimman
managartan dabarun cusa manufar “kawar da
qarancin shekarun da ke daqile matasa daga
takarar muqamai” ga ‘yan majalisa. Sauran
muhimman dabarun da aka yi amfani da
su, sun haxa da bayar da horo kan dabarun
sadarwa don inganta ayyukan isar da saqo,
tare da bayar da horo kan yadda ake gudanar
da tattaunawa a kafofin yaxa labarai.
Hukumomin NDI da USAID, sun shawarci
qungiyar YIAGA kan ta rubuta wasiqar aike
wa da saqonni ga kowace majalisar dokoki da
ke jihohin qasar nan. Ta hannun jami’inta na
jiha, inda za ta bijiro da manufar yin gyara ga
kundin tsarin mulki, sannan sai ta bi kadin
sakamakon martanin ‘yan majalisu daban-
daban.
A matakin qarshe na yaxa manufa, qungiyar
YIAGA ta yi matuqar roqon Shugaba Buhari
ta kafofi da dama, waxanda suka haxa da
tattakin zuwa fadar shugaban qasa, tare da
fafutika ta kaitsaye, inda aka tuntuvi jami’an
gwamnati kan su roqi shugaban qasa ya
amince don tabbatar da dokar.
Kasancewar qudurin ya samu rattaba hannun
amincewa a matsayin doka, sai fafutikar yaxa
manufar ta sauya salo zuwa “shirye ake da yin
takara – Ready to Run” don taimakawa wajen
horar matasan ‘yan takara su shiga zaven
2019, ta yadda za a bayar da dama ga matasan
da suka kai qudurin kan teburin shugaban
qasa su yi jagoranci don cin gajiyar fafutikar
da suka yi da aiki tuquru ba dare, ba rana.
Shugaba Muhammadu Buhari yan rattaba hannun tabbatar da dokar
rage yawan shekarun takarar muqaman siyasa a Mayun 2018 a gaban
matasan da suka yi fafutika
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
13