Magama Disamba 2018/Janairu 2019 | Page 14

Shirin baje-kolin kwaleji na EducationUSA 2018 daga Fatima Musa Lawan da Anjolaoluwa Akinmade – mahalartan EducationUSA Lagos S Jerin mahalartan nunin manyan makarantun Amurka a cibiyar MUSON akamakon yawan tattaunawar da aka yi an samar da ximbin bayanai. Wannan kuwa duk yana d anasaba da shirin baje-kolin ilimin kwaleji na qasar Amurka na shekarar 2018 da aka daxe ana jiransa, wato wanda a Ingilishi ake yi wa laqabi da 19th EducationUSA Annual College Fair. An gudanar da baje-kolin ne a tsakanin 24 zuwa 27 na Satumbar 2018 a Cibiyar MUSON da Gidauniyar ilimi ta Supreme Foundation da ke Legas cikin kwanaki biyu, inda daga bisani aka koma Abuja, inda aka sake shafe wasu kwanki biyun a Otal xin Sheraton da wasu manyan makarantun sakandare biyu, wato Loyola Jesuit College da International High School. Wakilan kwalwejoji 43 na Amurka, waxanda ake shafe tsawon shekarun da suka kama daga biyu zuwa huxu ana karatu a cikinsu suka samu halarta, waxanda suka haxa da Kwalejin Monroe da Jami’ar Kudancin Alabama da Jami’ar Drew University and Bucks County. Xalibai da malaman da suka wakilci makarantun sakadanraen gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya, sun fito ne daga kwalejin Queen’s College da Louisville 14 Wasu masu aikin sa-kai a baje kolin ilimi na EducationUSA da suka taimaka wajen samun nasarar shirin Girls High School da Sakandaren Corona da Kwalejin Kings College da Kwalejin Loyola Jesuit College da sauran makamantansu. . A wannan shekarar, karon farko, Legas ta gudanar da baje-kolin ga waxanda suka kammala karatun digirin farko bisa la’akarin da yawan tuntuva da ake ta yi game da sahihan bayanai kan karatu a qasar Amurka. Baje-kolin kwaleji da aka gudanar na kwanaki huxu ya bayar da dama mai qayatarwar ban mamaki ga xalibai da malamai, tare da sauran masu bayar da shawara kan harkokin ilimi wajen samun qarin fahimta game da yadda ake neman halartar manyan makarantun qasar Amurka. Jami’an da ke bayar da gurbin karatu sun yi musayar bayanai kan tallafin kuxi da jami’o’in ke bayarwa, tare da nagartar da ta fifita kowace jami’a. Sannan xalibai sun fahimci ximbin alfanun qwarewar aiki da ke tattare da karatun Amurka. A kowace rana ana fara baje-kolin ne da qarin haske ga mahalarta, inda aka gabatar musu da ximbin alfanun da ke tattare ilimin MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019 Amurka. Rukunin tsofaffin xaliban da suka halarci manyan makarantun Amurka da jami’an samar da gurabern karatu sun gabatar da jawabai kan muhimmancin ilimi mai zurfi da qimar mutuntaka da fa’idojin da ke tattare da jami’o’in Amurka. Daga nan sai aka kasa tarukan zuwa qananan manhaja har guda biyar kan matakan yin karatu a Amurka da samun izinin shiga Amurka a matsayin xalibi/xaliba bayan rukuni- rukunin tarukan sun karkasu, sai jami’an samar da guraben karatu suka samu damar ci gaba da ganawa da masu neman halarta jami’o’i sama da 4,000 don yin digirin farko da na biyu zuwa sama, waxanda suka halarci xaukacin wuraren. Irin qoqarin da aka yi wajen shirya muhimmin taro kamar na baje-kolin ilimi EducationUSA a Najeriya na da yawa, amma qimarsa ta cancanci yin hakan. Xaukacin mutanen da suka halarci baje- kolin makarantun ilimin Amurka na EducationUSA sun yi matukar yabawa da sambarka kan qoqarin da aka yi wajen samar da bayanai kan ximbin damar da ke tattare da karatun ilimi mai zurfi a qasar Amurka.