Magama Disamba 2018/Janairu 2019 | Page 15

Makoko Ganawar Jakada Symington da ‘yan makarantar da shugabannin al’umma ta jadadda muhimmancin ilimi R anar 4 ga Nuwambar 2018, Jakadan Amurka W. Stuart Symington ya ziyarci al’ummar Makoko da ke Legas. A lokacin ziyarar, ya gana da Daraktan shirin ‘Makarantar marasa galihu a Afirka – Slum2School Africa’, Mista Otto Orondaam, mai qwarewar sanin makama mai taken ‘2016 Mandela Washington Fellow’ yace ‘Makarantar marasa galihun Afirka na Slum2School Africa” aikin sa-kai ne qarqashin qungiyar da bsa ta gwamnati ba, wadda ke samar da kayan aikin koyarwa da kula da lafiya, ta hanyar saisaita tunani da kyautata zamantakewar qananan yara ‘yan makaranta a Makoko. Jakada Symington ya gana da qananan yaran da ke qarqashin kulawar shirin Makarantar marasa galihun Afirka na Slum2School, inda buqaci sanin sana’ar da suke son qwarewa a kai nan gaba a rayuwa. Sannan ya qara jadadda muhimmancin ilimi, tare da samun horon qwarewa a sana’o’in hannu da aikin sa-kai. daga Ibrahim Aliyu “Ba wai kuna koyon karatu ba ne a qashin kanku kawai ba; kuna koyo ne don amfanin xaukacinmu. Wani daga cikinku zai iya gano maganin wata cuta. Wani kuwa zai iya samar da dabarun shawo kan warware rikicin manoma da makiyaya, ta hanyar qarfafa musu gwiwa su zauna da juna cikin lumana,” inda ya bayyana haka a ganawarsa da ‘yan makarantar. Sannan ya gana da shugabannin al’ummar Makoko, inda daga bisani aka kewaya dashi a cikin kwale- kwale zuwa maqwafta. Makoko yanki ne na marasa galihu da ke gavar tekun Legas, inda gidaje da shaguna da coci-coci suke kafe tsororo bisa ruwan teku. A al’adance, muhimmiyar sana’ar mutanen wajen ita ce kamun kifi ko kuma al’amarin da ke da alaqa da sana’ar su. Shirin makarantar marasa galihun Afirka na Slum2School yana taimakawa wajen kyautata makomar qananan yaran dake cikin wannan al’ummar. Da yake bayanin kan dalilinsa na kai ziyara ga al’ummar Makoko, Jakada Symington ya ce, ‘Wannan wani mafi kyawun lokaci ne; yayin da mutane ke ta tattaunawa bisa ga harkokin siyasa, na ga dacewar nazarin halin da mutane ciki, tare da makomar matasa. Ba wai kawai manufata in nuna fifikon ilimi ba, har ma da cewa ina son jadadda muhimmancin ximbin dabarun koyon karatu ga mutane.” Jakada Symington lokacin da yake Magana da yaran ‘yan makarantar Makoko, inda jami’in shirin makarantar marasa galihu naSlum2School Otto Orondaam ya zuba ido MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019 15