LEGAS
Bikin fasahar Ake da baje-kolin
litattafai na 2018 a Legas
daga Temitayo Famutimi
Jami’in hulxa da Jama’a na Ofishin Jakadanci ke jawabi a wajen buxe biki
O
fishin Jakadancin Amurka
a Najeriya ya tallafa wa
bikin nunin fasaha da
baje-kolin littattafai na
Ake a shekarar 2018 a Legas. A
zagayowar bikin na shekara ta shida,
wannan shekarar an yi wa bikin
laqabin “Makoma mai qayatarwa –
Fantastic futures,” wanda aka gudanar
a tsakanin 25 zuwa 28 ga Oktoba.
Bikin na shekara-shekara ya baje
managartan rubuce-rubucen adabin
Afirka da waqe da kaxe-kaxe da raye-
raye, da fina-finai da dandamalin
wasannin dave. Marubutan Amurka
goma sha uku ne suka samu halarta,
waxanda suka haxa da Elizabeth
Bird da Farfesan kayayyaki masu
daxaxxen tarihi (Anthropology)
daga Jami’ar South Florida; da Mona
Eltahawy, marubuciyar maqala da
ke zaune a birnin New York-da mai
gabatar da jawabai kan harkokin
duniya Nnedi Okorafor, marubucin
qagaggen labari da littafinsa ya
tava lashe kyautar gasa da Farfesa a
Jami’ar Buffalo; da Tochi Onyebuchi,
marubucin mashahurin littafin nan
mai taken “Beasts Made of Night.”
Sannan akwai Jakadan Amurka kan
Jakadan Fasaha na Amurka day a kawo ziyara, Wanjiru Kamuyu lokacin varje guminsa a
fagen rawa
16
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
harkokin da suka danganci al’adu
Wanjiru Kamuyu wanda ya taka
rawa, “Portrait in Red,” a wajen bikin.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen
buxe taron, Jami’in hulxa da Jama’a
na Ofishin Jakadancin Amurka,
Russell Brooks ya nuna sha’awarsa
game da basirar qirqirar ‘yan Najeriya
a fannoni daban-daban. Bikin buxe
taron ya samu halartar Mataimakin
Shugaban qasar Najeriya Farfesa
Yemi Osinbajo, tare da ximbin
jami’an difulomasiya da ximbin masu
basirar qirqireqirqire. Masu fasahar
da suka kawo ziyara sun shiga cikin
‘yan makaranta sun gwamutsa don
zaburar da matsa su qara qwazon
tabbatar da cikar burinsu.
Jami’ar shirya bikin, Lola Shoneyin
tsohuwar mai halarta shirin horar
da marubuta da gwamnatin Amurka
ta xauki nauyi qarqashin shirin
Marubutan Iowa.
Jami’ar shirin Lola Shoneyin ta tava
halartar shirin horar da marubuta da
Gwamnatin Amurka ta xauki nauyi,
na marubutan Iowa.
Jerin manyan baqin da suka haxa da Mataimakin Shugaban qasa Farfesa Yemi Osinbajo da
Jagoran shirya bikin nunin Fasaha na Ake Lola Shoneyin (can quryar hagu)