Gasar hotunan NaijaGEMs a Legas
B
daga Russell Brooks
ikin nunin hotuna karo na 9 da
aka gudanar a Legas bana ya samu
halartar masu ayyukan fasahar 22
daga qasashe 18, inda aka yi masa
laqabin “Zamani ya shuxe,” Sannan, a karo
na farko mata ne suka mamake bikin inda
ka samu mata huxu da suka qware a harkar
alkinta kayan tarihi: wato Eva Barois De
Caevel da Wunika Mukan da Charlotte
Langhorst da Valentine Umansky, waxanda
ke da aniyar binciken bambance-bambancen
da suka baibaye al’umma tsawon zamani.
This year’s 9th edition of the Lagos Photo
Festival drew 22 artists from 18 countries
under the theme, “Time Has Gone.” In
addition, for the first time, the festival was
female-dominated featuring four female
curators: Eva Barois De Caevel, Wunika
Mukan, Charlotte Langhorst, and Valentine
Umansky whose intent was to investigate the
diversity that time encompasses.
Bikin da aka gudanar a tsakanin 27 ga
Oktoba zuwa 15 ga Nuwambar bana,
Gidauniyar masu ayyukan fasaha ta Afirka,
wato African Artists Foundation, tare da
xaukar nauyi daga cibiyar Mike Adenuga
da cibiyar nazarin fasalin qasashe ta
Amurka, wato National Geographic, U.S. da
ofishin Jakadancin Amurka da ke Legas da
Hukumar Al’adu ta Birtaniya da Gidauniyar
Ford Foundation.
Bikin nunin hotunan na Legas ya shahara
wajen bunqasa ci gaban ilimi da hotunan
zamani a Afirka, ta hanyar bayar d ahoro da
musayar al’adu a tsakanin ‘yan qasa da masu
fasaha a faxin duniya. Bikin nunin hotunan
na Legas na alfahari da kasancewsa bikin
fasahar baje hotuna na duniya na farko a
Najeriya.
Bisa gamsuwar ofishin jakadancin Amurika
da bikin, sai ya shigar da gasarsa ta xaukar
hotunan wurare masu qayatarwa, wadda ka
yi wa laqabi da NaijaGEMs. Tattara hotuna
50 masu qayatarwa da ke nuni da mafi
kyawun yanayin wasu wurare a Najeriya, ya
tabbata ne sanadiyyar zaven da aka gudanar
a shafukan sadarwar intanet na gasar da
Ofishin Jakadancin amurka a Najeriya ya
xauki nauyi.
Ita kanta gasar Jakada Stuart Symington
ya fito da ita, sakamakon ziyarar day a kai
xaukacin jihohi 36 na Najeriya. Shi ya sa
y ace ya kamata ‘yan Najeriya da dama
su samu irin damar d aya samu na kallon
wurare masu ban al’ajabi da qayatarwa a
Najeriya, waxanda suka haxa da rowan da
ke qwarara daga kan tsaunuka da hauhawar
tsirin duwatsu da nmun daji da tsirrai.
Domin a cewarsa duk wanda ya gani sai
ya cika da mamaki har ya furta cewa “Iye.”
Gasar NaijaGEMs ta bai wa ‘yan najeriya
masu sana’ar xaukar hotuna damar fito da
qimar qawata Najeriya, inda za suka sujha
kallo tare da sauran mutanen qasarsu.
Jami’in Hulxa da jama’a na Ofishin
Jakadancin da ke Legas, Russell Brooks ya
bayyana uirin tallafin da ofishin jakadancin
ke bai w amasu fasahar qirqire-qirqire da
cibiyoyin nazarin harkokin al’adu a Najeriya,
a wajen buxe bikin. Sannan ya yi nuni da
cewa gasar hotuna rta NaijaGEMs za ta
kawo managarcin sauyi game da labarin
Najeriya dangane da abubuwan ban mamaki
da mutanen cikinta.
Jagoran shirya biki Azu Nwagbogu,
da Charlotte Langhorst sun zuba ido
lokacin da Jami’in Hulxa da jama’ar
Ofishin Jakadancin Amurka, Russell
Brooks ke gabatar da jawabi
An fara baje-kolin NaijaGEMs a Abuja
cikin watan Yuli a kan tulluwar ‘Thought
Pyramid.’ Waxanda suka lashe gasar sun
karvi kyaututtukansu, sannan hotuna 50
mafi qayatarwa an bajekolinsu tsawon mako
guda.
Mataimakin
Daraktan Gidauniyar
masu Fasahar Afirka
(AAF), Charlotte
Langhorst ke yi
w amasu saurare
jawabi
A kodayaushe manufar ofishin Jakadancin
Amurka ce ya baje waxannan hotuna su
yaxu a wurare da dama, ta yadda za a samu
damar sake baje wasu hotunan a wasu sassan
qasar nan. Bikin baje-kolin hotuna na Legas
kafa ce da ta bayar da irin wannan damar.
CROSSROADS | December 2018/January 2019
17