Kafar Yaxa Ra’ayin
Al’ummar Qasa
daga Aisha Shehu
N
ajeriya ta kasance qarqqashin
jagorancin tsofaffin mutane
(tsawon zamani) duk da
qaruwar ximbin matasa a cikin
al’ummarta. Ana dai da tabbacin cewa
lamarin ba ya rasa nasaba da rashin sha’awa
ko rashin shigowar matasa a harkokin
mulki. Kodayake, shafukan sada zumunta
na intanet da kafofin sadarwar intanet
tasirinsu ya yi matuqar qaruwa, inda ximbin
matasa ke amfani da kafofin don bayyana
ra’ayinsu game da harkokin mulki, lamarin
da ya zama wani qalubale ga matsayin da
ake ciki. Qarfin farmakin da waxannan
kafofi suka kai wajen yaxa manufofi/bayyana
ra’ayi ya tursasa jami’an gwamnati sun riqa
mayar da martani, saboda matsin lambar
al’umma; don sun yi tasirin wajen yaxa
gaskiyar lamurra qeqe-da-qeqe a tsakanin
zavavvun jami’an gwamnati; sun kuma fitar
da managartan sahihan labarai da bayanai ga
ximbin matasan da ke hulxa da su, ta hanyar
bijiro da muhawarar da ke haifar xaukar
matakin yin aiki a aikace.
Wata mashahuriyar manufa da aka fi
kururutawa ta kafar shafukan intanet ta
“kawar da qarancin shekarun taikarar
muqamai ga matasa, wato Not Too Young to
Run’ lamarin day a haifar da gyaran kundin
tsarin mulki kan shekarun da suka cancanta
18
a yi takarar muqamai. Kwakwazon manufar
qungiyar ta ja ra’ayin al’umma a tsakanin
matasa da ke fafutikar dimokuraxiyya da
jagoranci nagari, an samu tabbacin hakan
ne yayin da ximbin waxanda suka yanki
tikitin tsayawa takara zavukan fitar da
gwani a Satumbar 2018. Ta kuma bayyana
qarara yadda tasirin matasa ke ta qaruwa
wajen yaxa ilimi da samun qarin fahimta a
shafukan sadarwa inda suke baje ra’ayoyi da
manufiofi, al’amarin da ke nuni da qaruwar
ximbin al’ummar qasa da suka shigo
harkokin siyasa don a dama da su.
Bisa la’akari da al’amuran ne, Gidauniyar
Aspilos, tare da tallafin Ofishin Jakadancin
Amurka, suka buqaci ganawa da ‘yan qasa
waxanda shekarunsu suka kama daga 18
zuwa 35 a qarqashin shirin kafar yaxa ra’ayin
’yan qasa’ Tallafin shirin an yi ne don cimma
manufar ofishin jakadancin na qarfafa
cibiyoyin dimokuraxiyya ta hanyar shigowar
al’ummar qasa da qungiyoyin fafutikar
haqqoqin al’umma ka’in da na’in a dama da
su. An gudanar da gwajin shirin da matasa
kimanin 1000 a Jihar Kano, inda jami’an
gidauniyar suka bayar da horo kan damawa
da ‘yan qasa ka’in da na’in da dimokuraxiyya
da jagoranci nagari, kan doron aiwatar da
ayyuka a aikace don bunqasa managartan
tsare-tsaren dimokuraxiyya a lokacin
zavukan shekarar 2019.
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
Shirin xungurungum an tsara shi ne don
qarfafa wa matasa gwiwa su taimaka wajen
tabbatar da gaskiya a tsarin ayyukan zave,
wajen ganin an gudanar da shi cikin lumana
da tsaftar nagarta da adalci. Sannan shirin
zai gana da masu ruwa da tsaki, waxanda
suka haxa da hukumomin tsaro da masu
yi wa qasa hidima (NYSC) da qungiyar
shugabannin qananan hukumomi da
cibiyoyin gargajiya da na haxakar addini,
haka kuma da qungiyoyin da ke da matuqar
tasiri a cikin al’umma, waxanda suka haxa
da qungiyar direbobin mota (NURTW) da
qungiyar matan da ke hada-hadar kasuwanci
a kasuwanni (MWA).
Baya ga muhimmiyar gudunmuwar
da aka bayar wajen bunqasa tafarkin
dimokuraxiyya a tsarin ayyukan zave, kafar
za ta sake yin tasirin kaitsaye wajen tantance
gaskiyar lamarin kan ayyukan jami’an zave.
Kafar yaxa ra’ayin ‘yan qasa mafuskantar
matasa ce da shekarunsu suka kama daga
18 zuwa 35 a xaukacin jihohi 36 da ke
faxin tarayyar Najeriya da za su riqa yaxa
ilimin jagoranci a tafarkin dimokuraxiyya,
tare da shigarsu hada-hadar harkokin
rayuwa kaitsaye. Tsararraki za su ci gaba
da baza bayanai don qarfafa dabarun bin
kadin gaskiya qeqe-da-qeqe daga zavavvun
wakilan al’umma, tare da koyon dabarun
tarairayar al’ummomi tun daga matakin
gidajensu ko karkararsu.