QUNGIYA
Babban taron YALI
na tabbatar da gaskiya
qeqe-da-qeqe
daga Diran Adegoke
Daga hagu zuwa Dama mai warware taqaddamar tattaunawa Dayo Benjamins-Laniyi
Babban baqo mai jawabi, Sentell Barnes Jami’in Kula da harkokin al’adu na ofishin
Jakadancin Amurka, Sterling Tilley, Babban Jami’in haxaxxiyar qungiyar fafutikar matasa ta
YALI (a ofishin Jakadancin Amurka da ke Legas), Austin Emeanua a lokacin babban taron da
aka gudanar a Abuja
R tarukan Majalisar xinkin Duniya, wanda
zai mayar da hankali kacokam wajen fito
da dabaru da ayyuka kan yadda matasa za
su taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen
samar da ximbin alfanun dimokuraxiyya ga
‘yan qasarta.
Babban taron YALI na tabbatar da gaskiya
qeqe-da-qeqe an shirya shi ne da manufar
cusa wa matasa dabarun fito da managartan
tsare-tsaren da za su yaxa manufar tabbatar
da gaskiya qeqeda-qeqe a wajen jagoranci
a matakin jiha da faxin tarayyar Najeriya.
Babban taron an kasa shi ne a rukunin
qwararru da bayar da horo da tsarin fasalin Da yake jawabi a wajen taron, Sterling Tilley,
Jami’in kula da al’adu na ofishin jakadancin
Amurka da ke Abuja, ya ce, “rukunin
qungiyoyin da ke qarqashin YALI, rukuni ne
na matasan Najeriya, waxanda ba wai kawai
maganganu suke yi ba, har ma da aiwatar
da aiki a aikace. Wannan shi ne dalilin da
ya sanya Ofishin Jakadancin Amurka ke
alfahari da tallafa wa babban taron don a ji
qarajin muryoyinku, sannan a ga aikinku
qarara don tattauna a matakin qasa.” Kuma
Mista Tilley ya yi amfani da damar taron
wajen qaddamar da shirin faxakarwar
rukunin qungiyoyin YALI kan masu kaxa
anar Talata 4 ga Satumbar 2018,
wakilan qungiyar horar da
jagororin Afirka ta YALI suka
taru a Abuja don babban taro kan
tabbatar da gaskiya qeqe-da-qeqe. Babban
taron dai shi ne irin sa na farko da qungiyar
ta gudanar tun bayan kafuwarta a shekarar
2014. Qungiyar YALI a Najeriya tana da
‘ya’yan qungiya sama da 120,000, waxanda
ke da manyan cibiyoyi a jihohi 23, tare da
wasu manyan cibiyoyi bakwai da ake shirin
buxewa nan da makonni masu zuwa.
8
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
quri’u a Najeriya, wanda aka yi wa laqabi a
Ingilishi da “NaijaVotes”, wani jerin shirye-
shiryen ilimantarwa da faxakarwa ta kafar
sadarwar intanet d ata mutum a qashin
kansa, wadda aka tsara da nufin fahimtar
da ‘yan’yan qungiyar kan yadda za su shawo
kan damuwar masu kaxa quri’a ko sayen
quri’u, tare da yaxa bayan qarya da kalaman
cusa qiyayya da tashe-tashen hankulan
lokacin zave. A daidai lokacin da ‘yan
Najeriya ke shirin tunkarar manyan zavukan
qasa da ke qaratowa.
An kammala babban taron ne a ranar
Alhamis 6 ga Satumbar 2018, inda aka
fitar da jerin muhimman al’amuran da aka
cimma matsaya kansu, har 47, waxanda za
su shawo kan matsalolin da suka haxa da
kula da lafiya da ilimi da tsaro da kasuwanci
da zuba jari; al’amuran da za a gabatar wa
gwamnati da kafafen yaxa labarai.