Magama Disamba 2018/Janairu 2019 | Page 7

DANGANTAKAR AMURKA DA NAJERIYA DANGANTAKAR ZAVEN OSUN da mafi girman kadarar Najeriya J akadan Symington ya sha faxa a lokuta da dama cewa babbar kadarar arzikin Najeriya ba ximbin manfetur da ke shimfixe a qasa ba ce, domin ba ta da wasu ximbin albarkatu (ko ma’adinan) da suka wuce mutanenta – ximbin manyan albarkatun Najeriya. Kasancewar hakan bata tabbata a gareni ba, sai a zaven 22 ga Satumba, inda aka gudanar da zaven gwamna a Jihar Osun, yayin da ximbin masu sa-ido suka himmatu wajen ganin an yi zave mai tsafta, cikin adalci da nagarta, ba tare da wani tashin hankali ba a lokacin gudanar da zave. Lokacin da na kasance a Jihanar Osun ranar zave, a qashin kaina na shaida yadda xaruruwan ‘yan Najeriya suka himmatu wajen bayar da gudunmuwarsu, ta hanyar sa-ido wajen kai dimokuraxiyyar Najeriya ga gaci, inda qungiyoyin fafutikar haqqin al’umma daban-daban suka halarta, waxanda suka haxa da qungiyar fafutikar bunqasa rayuwar matasa ta Afirka, wato “YIAGA Africa” da Cibiyar fafutikar aiwatar da tsare-tsare bisa doka ta “PLAC”, sai matattara qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma, da Gidauniyar CLEEN, wato daga Benjamin Williams kaxan ken an daga cikinsu. A vangarenmu kuwa,Amurka ta tura ma’aikatan ofishin jakadanci 52 da suka halarci zaven Osun na ranar 22 ga Satumba. An yi rukuni takwas na jami’an sa-ido na duniya duniya, waxanda suka karaxe sassan jihar a ranar zave, kuma sun ziyarci qananan hukumomi 30, inda suka tsaitsaya a kusan rumfunan zave 300 daga jerin rumfunan zaven jihar 3,010 don sa-ido kan yadda aka kaxa quri’u tare da qirgar sakamako. Tawagarmu ta sa-ido ta yi haxin gwiwa da sauran ofisoshin jakadanci na duniya, waxanda suka haxa da na Tarayyar Turai (EU) da Birtaniya, don faxaxa ayyukan sa- idon al’ummar duniya. Sai dai duk da haxin gwiwarmu da al’ummomin duniya, mun samu kaiwa ga kashi 10 cikin 100 kawai na xaukacin rumfunan zaven Jihar Osun. Wannan na nuni da ximbin muihimmancin ‘yan Najeriya masu sa-ido a ranar zave. Dubban masu aikin sa-ido daga qungiyoyin fafutikar haqqoqin al’umma, ‘yan Najeriyar da suka yi aikin sa-ido sun karaxe wurare da dama da masu sa-ido na ofisoshin jakadancin qasashen duniya. Masu aikin sa- ido ‘yan Najeriya ba aikin sa-ido kawai suka yi a rumfunan zave ba, har ma da kawar da munanan al’amuran da ka iya hargitsa zaven suka yi. Sun bi kadin yadda aka qirga quri’u, sannan suka miqa rahotonsu ga qungiyar bunqasa rayuwar matasa ta Afirka YIAGA, waxanda a ka jera a jaddawalin alqalumanta na “PVT” wanda ya yi bibiya da nazarin bisa la’akari da rahoton ‘yan qasa da suka aikin sa-ido, don qimanta yadda ya dace sakamakon zaven ya kasance. Kamar yadda kuke iya yin hasashe, tsarin jaddawalin alqaluman PVT kariya ne ga duk wata qumbiya-qumbiyar jirkita sakamakon zave, saboda YIAGA da masu aikin sa’ido a qarqashinta sun samar da hanya mafi inganci mai cin gashin kanta don tantance sashihancin sakamakon, yadda za mu iya kwatanta sakamakon da jami’an hukuma suka fitar. ‘Yan qasa masu aikin sa’ido da jaddawalin PVT na bayar da muhimmiyar kariya ga dimokuraxiyyar Najeriya da ke tasawa. Hatta a tsakankannin qasashen duniyar da dimokuraxiyyarsu ta daxe tana gudana, babu zaven da babu tangarxa. Muhimmin abu dai, shi ne nagartar zavukan Najeriya su ci gaba da wanzuwa don samun qarin inganci a duk lokacin da zave ya zagayo. Da za a iya qara inganta nagartar zavuka a Najeriya, ta samun qarin masu fitowa don kaxa quri’a, sannan a zaburar da ‘yan qasa su shigo a dama dasu a dimokuraxiyyarsu da ke samun karsashin qarfafawa. Da zarar an samu qarin masu kaxa quri’u, to da wuya miyagu su damalmala dimokuraxiyyar da tashe-tashen hankula ko tauye haqqoqi da sayen quri’u ko satar akwatin zave. Nazarin lamarin a tunnin zuci, daidai lokacin da zavukan qasa na shekarar 2019 ke qaratowa, ina shawartarku da ku yi amfani da katin zavenku don tabbatar da ’yancinku na yin zave. Kuma idan kun ga ‘yan qasa da ke aikin sa-ido a rumfar zavenku, to ku yi musu godiya bisa la’akari da gudunmuwar da suka bayar don kare dimokuraxiyya. Ku tuna cewa ku ne mafi kyawun nagartar albarkatun Najeriya. Yin zave haqqinku ne – da Fabrairu ya zo, a fito don kaxa quri’a! Wani nakasasshe ya yi hoto da jami’in sa-ido a wajen zave daga Ofishin Jakadancin Amurka, ben Williams, lokacin d ayake kaxa quri’arsa MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019 7