xauki alqawuran tabbatar da zaman lafiya
ga al’umma. Wakilan Amurka sun bijiro
da buqatar ganin kawo xauki ga waxanda
suka cancanci kaxa quri’ar da ke fama da
matsalolin rayuwa, waxanda suka haxa da
mata da matasa da waxanda musifar yaqi
ta tarwatsa su daga gidajensu da nakasassu
(ko masu buqata ta musamman).
Qungiyar sa-kai ta Zave–
Ba–Faxa–Ba ne ta goyi
bayan matsayin Amurka na
ganin an yi zave mai tsafta
da adalci da gaskiya tare da
jawo kowa a jika a zavukan
2019
mahangar tsare-tsaren da za su ciyar da
qasa gaba. Jami’an gwamnatin Amurka
sun gana da masu ruwa da tsaki a harkar
zave, don jadadda muhimmanci. Don
kai ga gacin cimma manufar ofishin
jakadancin ya tallafa wa Hukumar zaven
qasa a qoqarinta na tafiya a salon ci
gaban zamani, wajen inganta qwarewar
ma’aikatanta.
Tattaunawar ta qara faxaxa ne da jami’an
Hukumar Zave, inda aka yi nazari kan
shirye-shirye da aiwatar da ayyuka wajen
gudanar da zaven 2019, kuma jami’an
Amurka sun gana shugabannin siyasa da
wakilqan qungiyoyin fafutikar haqqin
al’umma don tattaunawa kan damuwar
da ake da ita na tashe-tashen hankula,
sannan aka qarfafi gwiwar ‘yan siyasa su
Mataimakin Shugaban Ofishin Jakadanci,
David Young shi ya jagoranci tawagar masu
sa-ido a zaven Jihar
6
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
Fahimtar cewa kakar zaven da ba ta
nasaba da tashin hankali yana da ingancin
da ke hana kange kowane xan/‘yar qasa ya/
ta shiga a dama shi/ita a harkokin zave,
ba tare da barazana game da daidaituwar
harkokin qasar, don haka ofishin
jakadancin ya jawo jakadu masu manufa
irin wannan don jadadda buqatar ganin an
yi zavuka cikin lumana.
Tunda kafafen yaxa labarai na da matuqar
muhimmanci wajen samar da sahihan
bayanai da za su taimaka wa ‘yan qasa
wajen tunanin yanke matsaya. Ofishin
jakadancin Amurka ya bayar da tallafi ga
‘yan jarida. An samar da bayanai masu
nasaba da zavuka, inda aka gudanar
da taron bita da sanin makama ga ‘yan
jarida (da jami’an yaxa labarai), waxanda
aka zavo da gidajen talabijin da rediyo
da jaridu da kafofin sadarwar shafukan
intanet a xaukacin faxin Najeriya. Ofishin
jakadancin akai–akai yana fafutikar
ganin an kauce wa cin zarafin ‘yan jarida
ko masu fafutika a kafofin sadarwar
intanet da masu baje bayanai a shafukan
saedarwar ko takura wa masu gudanar da
taruka da zanga-zangar lumana.
Hasashen zavukan shekara ta 2019
Shugaban qasa Muhammadu Buhari
na Jam’iyar APC zai fafata da tsohon
mataimakin shugaban qasa Atiku
Abubakar na Jam’iyyar PDP, inda zaven
zai kasance mai zafi. Shin zaven zai
kwata yadda ta kasance a zaven shekarar
2015 al’amarin da ake ganin sabo ne, ko
kuwa tsarin ya tabbata ne don kauce wa
tashintashina a qasar da tarihin siyasar
ta ke xamfare da rikici? A wannan qasa
da ta zama manuniya, kuma mafi qimar
arzikin dimokuraxiyya, zaven 2019 zai
zama zakaran gwajin dafi, wajen auna irin
jajircewar gwamnati tabbatar da gaskiya
qeqe-da-qeqe kan al’amuran da suka shafi
kafuwar dimokuraxiyya.