KAFA CIBIYOYIN
BUNQASA
DIMOKURAXIYYA
MASU QARFI
A ZAVUKAR 2019
daga Mirna Torres
Z
avukan Najeriya na shekarar
2015 su ne mafi tsaftar nagarta
da aka gudanar cikin lumana,
tun bayan dawowar mulkin
qasar kan tafarkin dimokuraxiyya a
shekarar 1999, lamarin ya haifar da miqa
ragamar mulki daga hannun gwamnati
mai ci zuwa hannun jam’iyyar adawa
tsawon tarihin qasar. Don haka Amurka
ke da zaquwar ganin ta tallafa wa Najeriya
wajen kafawa da faxaxaw ximbin alfanun
dimokuraxiyya a zavukan da ke qaratowa
na shugaban qasa da mataimakin shugaban
qasa da na ‘yan majalisar dokokin qassa
da gwamnomi da na mataim, akan
gwamnomi, har ma da na xaukacin ‘yan
majalisar dokokin jiha a shekarar 2019.
Mutanen Najeriya na aiki tuquru wajen
kafa qarfafan cibiyoyin dimokuraxiyya.
Kuma ofishin harkokin difulomasiyar
jakadancin Amurka a Najeriya na matuqar
tallafawa wajen cimma wannan manufa.
A matsayinta na mai sa-ido bisa adalci
da qarfafa tsarin zaven da babu son rai
a cikinsa, Amurka na qoqarin qarfafa
gwiwar masu kaxa quri’a, don tabbatar
da nagartan zavuka. Daqile tashe-tashen
hankula (ko rikici) lokacin zave, wani abu
ne da ya kamata a kula da shi, don shi ne
jigon tabbatar da nagarta da daidaiton
adalci, tare da bunqasa dimokuraxiyyar
Najeriya.
Najeriya ta cancanci zave mai tsafta
da nagartar adalci da ke yi qeqe-da-
qeqe, wajen ganin an gudanar da zave
cikin lumana, al’amarin da zai tabbatar
da kafuwar turakun cibiyoyi masu
inganci. Don cimma wannan manufa,
ofishin jakadancin Amurka a Najeriya
na aiki kafa-dakafaxa da sauran sassan
difulomasiyar ofisoshin jakadancin
qasashe da qungiyoyin fafutikar haqqin
al’umma, da Hukumar Zave ta qasa
(INEC) tare da sauran jam’iyyun siyasa
wajen ganin an gudanar da zave mai
inganci cikin lumana.
Amurka da masu ruwa da tsaki a harkar
zave
Bisa la’akari da qimar muhimmancin
siyasa da tattalin arzikin Najeriya a Afirka
da faxin duniya, muhimmanci zavukan
d ake qaratowa nagartarsu ta zama abin
(koyi da) doka. A bara, ofishin jakadancin
Amurka ya shawarci jiga-jigan ‘yan siyasa
dasu kauce wa tashin hankali, sannan
su bai wa masu kaxa quri’u kyakkyawar
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
5