Magama Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman | Page 8

DUTSEN RIYOM daga Rimamkongende Shamaki - @kongsshamaki Lamari ne mai qayatarwar banmamaki idan mutum ya yi tunanin yadda duwatsun suka cure wuri guda tsawon dubbanshekaru.Anadai yi musu laqabi da Beta Beta a harshen yankin, ma’ana “duwatsu qwar uku”. Curewar duwatsun na xaukar hankalin masu yawon bude ido a faxin duniya, kuma suna samar da kuxin shiga ga mazaunan yankin. Wani dattijon Riyom (al’ummar Berom) ya ba ni labari. A cewarsa, zamanin da suke tasowa (suna qanana) sun yi amannacewa Ubangijine ya halicci duwatsu. Wata daxaxxiyar al’adar mutanen yankin, ita ce yara Maza waxanda shekarunsu suka kama daga bakwai sukan je dutsen xauke da kwando don kama qwari. Sannan bayan sun soya sai su kaiwa dangin mahaifiyarsu. Danginsu za su ci qwarin, sai su bai wa yara mazan tukwicin kaza, inda sukan sanya musu albarka. Wannan dutsen dai har yanzu abin alfaharin jihar Filato ne. 8 MAGAMA | Nuwamba 2018 Fitowa Ta Musamman