Magama Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman | Page 7

N a tambaye shi kan yadda aka yi ya shiga harkar xaukar hoto, kuma lamarin na da matuqar ban sha’awa jin cewa ya fara ta’ammali da na’urar xaukar hoto ta Kyamara a matsayinsa na mai shirya fina-finai. Kasacewar haqiqanin gaskiyar lamari dabarun ayyukan ana iya amfani da su a xaukacin shirya fina-finai da xaukar hotuna, hasalima da wuya waxannan dabaru su yi hannun riga. Kongs dai ya yanke matsaya wajen bin wannan tafarki. Ya kasance yana buqatar koyon qarin dabarun haskaka hoto, fasaltawa da juya tabaron hango hoto, amma a wata hanya da kwalliya za ta biya kuxin sabulu ba tare a vata lokaci ba, fiye da yadda shirin fim ke xauka. Don haka ya yi kwas xin xaukar hoto. Cikin shekarar 2015, ya halarci wani kwas na watanni uku a Jami’ar Majalisar Xinkin Duniya a wani reshenta da ke Kona a tsibirin Hawaii Sanadiyyar wannan horo da ya samu ya zavi tattara hankalinsa sosai wajen hada-hadar xaukar hoto, duk yake ya riqa haxawa da shirya fina-finai. Kongs na zaune ne a Jos, Jihar Filato, kuma yana gudanar dabarun wurin shirya fim da xaukar hoto, sannan ya kasance mai xaukar hotunan fim sanye da tufafin zamani riga da wando da suka kame jiki, inda ya fi sha’awar xaukar hotunan jerin tsirrai da furannin kallo da hoton fito da cikakkiyar sura, ta yadda yakan surka da qawar al’ada. Littafin Teburin Shayin Gahawa (Coffee Table Book) da aka ba shi a matsayin kyautar lashe gasa, ya zaburar da shi wajen fara shirin tattara bayanai game da qabilun Filato. Tuni dai ya zuba kuxi don bunqasa al’umma mai tasowa da al’ummar da ya fito cikinta, inda a halin yanzu yake horar da matasan 10 Jos sana’ar’ xaukar hoto. Sannan yana koyar da kwamfuta a wata makarantar sakandare da ke Jos. Da yake nazarin kasancewarsa gwarzon da ya lashe gasar xaukar hotunan wurare masu qayatarwa na NaijaGEMs, Kongs ya ce, ya sam albarkar wannan sabuwar karramawa da aka yi masa, har ta kai ga waxanda bai ma sansu ba sukan tsayar da shi don su taya shi murna. Nasarar da ya samu ta qara masa qwarin giwar ci gaba da xaukar hotunan jerin tsirrai da furannin kallo, wani fanni na hoto da hada-hadar kasuwancinsa ba ta da wani qimar fifikon daraja, in an kwatanta da wasu fannonin na xaukar hoto. Sannan a cewarsa: Kowane lokaci a yanzu da nan zuwa gaba, wannan gasar na tunatar da ni kan yadda hoto guda kawai ya ba ni qimar darajar karramawa ta duniya.” Ta yiwu lamari mafi muhimmanci, yabon da ya tava samu kaxan ne, kuma ya xan tuntuvi wasu don neman shawarwari, al’amarin da ya haifar masa da samun nasara kaitsaye, ba ma tare da ambton babbar kyautar kymarar xaukar hoto samfurin Canon EOS 5D Mark 4 – kyamarar samfurin Canon’s DSLR lineup. Samun waxannan na’urori zai ba shi damar aiwatar da ayyuka ga abokan hulxarsa, waxanda kan xauke shi har zuwa Legas. A cewar Kongs “Tuni da na aiwatar da managarcin aiki da kowane irin nau’in kyamarori domin hotunan da ke fitowa suna da matuqar kyau. Ban ma tava yin amfani da na’urar kyamara mai nagartar da ta kai wannan ba.” Samun na’urar ya sanya ya xauki shirin fim mai taken Qiren Qarya (Falsehood), wanda ya shiga gasar shirya fina-finai ta ‘My Rode Reel.’ Muna haxa hannu ne don ganin cimma nasarar tallafawa da bunqasa fasahar matasa. Ba tare da la’akari da sakamakon wannan gasa ba, Mista Shamaki tuni ya kafu a matsayin gwarzo, wanda ko tantama babu, zai ci gaba da samun ximbin nasarori a nan gaba. Mahaifin Rimamkongende da sauran waxanda suka fafata a gasar suna taya shi murnar karvar kyaututtuka MAGAMA | Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman 7