MAFI QAYATARWA 10
TAFKIN IYAKE
daga Oluwatomisin Runsewe
- @roluwatomisin
Tsaunin Oke-Ado na nan a garin Ado
Awaiye da ke Jihar Oyo. A saman
tsaunin akwai tafkin Iyake, xaya daga
cikin tafkunan duniya da ke saman
tsauni da ya shahara. Yana nan a kan
nisan mita 150 a saman teku, kuma
akwai tafiyar sa’a biyu kafin a isa zuwa
sashen da yake a tsaunin. Mutanen gari
sun xauki tafkin a matsayin wuri mai
tsarki, har ma suna da yakinin cewa
ruwan tafkin yana maganin cututtuka.
Baya ga haka qayatarwarsa na da ban
mamaki, domin kasancewar tafkin a
saman tsaunin yana matuqar xaukar
hankali, kuma tsaunin Oke-Ado wuri
ne da masu yawon buxe ke kai-kawo,
da masu hawan tsauni da wajen yin
sansani, ga motocin da ke tafiya kan
zirin waya (cable cars) da suke haxa
al’ummar kewayen tsaunin.
kan tudun itatuwan gandun daji,
wanda nisan tsawonsa ya kai mita
458.3. Tsaunin Patti tsibi-tsibin
itatuwan gandun daji ne da ya
karaxe faxin kilomita 15, sannan
ana iya hango shi daga kowane
sashe na birnin Lokoja, babban
birnin Jihar Kogi. Tarihin kafuwar
Najeriya a matsayin qasa ba zai
cika ba, har sai an tabbtar da qimar
gudunmuwar wannan yanki wajen
qirqiro qasar nan.
KADARKON MAHAXAR KOGUNAN
BINUWAI DA NEJA
by Abalaka Philip Ejima
- @mruniverse_01
A wannan hoton, za ku iya ganin hamshaqin
kogin Binuwai, babbar jelar Kogin Neja,
tare da qayataccen kadarkon mahaxarsu
da aka hango daga kan tsaunin Patti da ke
Sa Frederick John Dealtry Lugard
tunanin kafa Najeriya ya bijiro
masa a kan tsaunin Patti inda daga
bisani ya cimma matsaya ya kafa
yankunan Arewaci da Kudanci
qarqshin kulawar kariyarsa.
Uwargida Flora Shaw Lugard ita
ta qirqiro sunan Najeriya (Niger-
Area) daga kan wannan tsauni,
bayan da ta kalli qayataccen
yanayin wajen. Wannan mahaxa
ita ce turakun mikiya da dawakan
tambarin Najeriya ke wakilta.
Fararen ziraye guda biyu da ke da siffar
harafin ‘Ya’ suka haxu, inda suke nuni da
mahaxar koguna biyu.
MAGAMA | Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman
15