RUWAN DUTSEN OLUMIRIN
daga Chukwudi Onwumere
- @Guzeartworld_photography
Makwararar ruwa ta Olumirin jikar Oduduwa Akinla ce ta ganota a
shekarar 1140 AD (Bayan Almasihu), wanda ya kasance tushen asalin
Yarbawa. Al’ummar wannan zamani sun xauki wannan makwararar ruwa
a matsayin wuri mai tsarki don tsarkake ruhi. Wuraren na nan a Erin-
ijesha, Jihar Osun, kuma wurin na xaukar hankalin ximbin masu yawon
buxe ido.
GARIN IDANRE
daga Omololu Aiyeola
- @olayode_fortune
Saman dutsen Idanre ya kai tsawon
qafa 4,000, a saman teku, tare da
ximbin tsirin duwarwatsu. Jerin
duwatsun da suka zagaye wannan
gari da aka nuna a qasa, kuma ya
samar wa makwaftan al’ummar
yanki wajen yawon buxe ido da
wuraren hutu.
14
MAGAMA | Nuwamba 2018 Fitowa Ta Musamman