SAQON JAKADA
W. Stuart Symington
Jakadan Amurka a Najeriya
Saqon Jakada Maraba da wannan fitowar ta
Magama
A daidai lokacin da mutanen Najeriya ke
tunkarar babban zave a shekara mai zuwa,
xaukacinmu da ke Ofishin Jakadancin
Amurka muna hanqoron ganin mun shaida
yadda za a gudanar da zaven hart a kai ga
ya samu nasarar da ta zarta wada aka samu
a zavukan shekarar 2015, waxanda aka
tabbatar da gudanarsu cikin lumana tare da
MAGAMA
Ana wallafa ta ne a bayan kowane wata
uku a sashen Hulxa da Jama’a na Ofishin
Jakadancin Amurka a Najeriya
TAWAGAR EDITOCI
Aruna Amirthanayagam
(Shugaba kan Harkokin Hulxa da Jama’a)
Russell Brooks
(Jami’in Hulxa da Jama’a a Legas)
Glenn Guimond
(Jami’in Aikin Jarida)
Olaoluwa Aworinde
(Edita da Daukar Hoto)
Xaukacin sakonni a aike ta
wannan adireshi:
Ga Editan, Mujallar Magama
Sashen Hulxa da Jama’a na Ofishin
Jakadancin Amurka
Plot 1075 Diplomatic Drive,
Central Business Area, Abuja, Nigeria
Tel: (09) 461-4000. Fax: 09-461-4305
OFISHIN LAGOS:
Ofishin Jakadancin Amurka
2, Walter Carrington Crescent, Lagos
Tel.: +234-703-150-4867/2444
E-mail: [email protected]
Website: ng.usembassy.gov
inganci da sahihanci.
A wannan fitowar, mun bayyana wasu daga
ayyukanmu na haxin gwiwa da ’yan Najeriya
don cimma managarciyar manufa. Mun
gana da jiga-jigan gwamnatin Najeriya da
manyan masu ruwa da tsaki a harkar zave da
shugabannin siyasa da qungiyoyin fafutikrar
haqqoqin al’umma, tare da xaukacin al’umma
waxanda za su kaxa quri’a a wajen zave. Xan
takararmu kawai shi ne tsarin gudanarwa.
Manufarmu ita ce taku; a tsarin da zai
kasance yin gaskiya qeqe-da-qeqe da nagarta
da tsafta da adalci da za su wanzar da zaman
lafiya. Zavukan da za su tabbatar da cikar
burin mutanen Najeriya.
Ziyarar kwanan nan da Mataimakin
Sakataren Harkokin Afirka na qasar Amurka,
Tibor Nagy ya kawo Najeriya, ta fito da irin
wannan manufa tamu. A ziyararsa ta kwanaki
biyu, ya gana da Shugaban Hukumar Zave ta
Qasa, da Sarkin Musulmi, Sultan na Sakkwato
tare da wasu jiga-jigan shugabannin
jam’iyyun siyasa. Muhimmin saqon da ya isar
ga kowa-da-kowa a cikin waxanda ya gana da
su, shi ne, kamar yadda na bayyana tun farko,
Amurka na mara wa xan takara guda baya ne
a waxannan zavuka, kuma shi (xan takarar)
ba wani ba ne, illa tsarin gudanar da zavuka.
Babu wani burin a qaqava wani mutum, ko
fifita buqatun wata jam’iyyar siyasa a kan
haqqoqin mutanen Najeriya da ke da ’yanci/
haqqin zaven wanda suke so ya jagorance/
shugabancesu.
Akwai ximbin masu ruwa da tsaki a zave.
Mafi muhimmanci su ne masu kaxa quri’a.
Kowane mutum da ya cancanci kaxa quri’a,
ya yi rajista da hukumar zave ta qasa (INEC),
kuma ya mallaki kazin zavensa/ta na
dindindin, don haka haqqi ne da ya rataya
a kansa/ta wajen tabbatar da an gudanar da
zave cikin lumana don tabbatar da cewa sun
kaxa quri’unsu an tattara an qirga. Da zarar
ka/kin aikata hakan tare da kowane xan/’yar
qasa a cikin al’ummarka/ki a xaukacin faxin
qasar nan, babu mugun/azzalumin da zai
hargitsa tsarin ya vata maka/ki makoma.
Sauke wannan xauyi zai sanya ka/ki zama
mai kare kyakkyawar makomar Najeriya,
tare da tabbatar da ’yanci da yalwar walwala a
faxin duniya da za ta amfanar da xaukacinmu
gaba xaya. A sha karatu lafiya.
Jakada W. Stuart Symington
A wannan fitowar
Babban Labari
Tarairayar mutanen
Najeriya
Shafi na 4
Shafi na 10
Qarancin
Shekaru ba ya
hana Takara
Zaven Osun
Shafi na 7
Shafi na 13
Babban
Taron YALI
Makoko
Shafi na 8
Shafi na 14
Dabarun Sabunta
Qarin Shiri
A biyo mu:
Shafi na 9
Bugu na 22 Lamba na 3
Gasar Hotunan
NaijaGEMs a
Legas
Shafi na 18
MAGAMA | Disamba 2018/Janairu 2019
3