Magama Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman | Page 5

Yadda al’amura suka wakana daga Joseph Adah & Olaoluwa Aworinde Daki-dakin yadda aka gudanar da gasar hotuna ta NaijaGEMs Shirin Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya na gasar xaukar hotunan abubuwa da wurare masu qayatarwa da aka yi wa laqabi da NaijaGems Jakada W. Stuart Symington ne ya fito da shi, sanadiyyar ziyarar da ya kai jihohi 36 na Najeriya, inda ya gane wa idonsa yanayin qasar mai ban sha’awa. Gasar ta bai wa ’yan Najeriya damar haska (wa duniya) irin kyawun qasarsu ta hanyar hoto mai qayatarwa, inda za su bayar da labari mai daxin ji don qarqfafa gwiwar al’ummar qasa su yi alfahari da shi. A cewar Jakadan, “A xaukacin faxin qasar nan (Najeriya) akwai wurare masu matuqar kyawun yanayi, waxanda suka haxa da wasu tsirrai da furani da namun daji na musamman, muhimman tsaunuka da koguna da ruwan da ke gangarowa daga kan duwatsu da da gine-ginen tarihi. Akwai abubuwan da Ubangiji ya halitta da waxanda mutum ya qirqiro daga wannan kusurwa zuwa wata kusurwa ta qasar nan. Muna son ku xauko hoton xaya daga wurare da abubuwan Najeriya masu ban sha’awa da matuqar qayatarwa, ta yadda kowane xan Najeriya da kowane mutum a faxin duniyar nan in ya gani zai cika da ban “MAMAKI.” Waxanda suka shiga gasar an kasa su rukuni-rukuni, ta hanyar samar da managartan hotuna na asalin wurare masu qayatarwa, waxanda kyawun yanayinsu ya kevanta da wani yanki ko jiha; wuraren da aka samu sun kasance tambarin tunqahon mutane ko abin alfaharin al’adar wannan jihar. An tura hotunan ne ta kafar shafukan intanet da suka haxa da Flickr da Instagram a tsakanin ranakun Juma’a 6 ga Afirilu zuwa Juma’a 4 ga Mayun 2018. Ofishin Jakadancin ya karvi hotunan shiga gasar 330. An xora wa wani kwamiti alhakin bibiyar nazarin hotunan da aka zavo, har aka tantance mafi nagarta guda 50. Waxnnan hotuna an baje su don al’umma su kaxa musu quri’a a shafukan sadarwar Facebook da Instagram na Ofishin Jakadancin. An kaxa quri’u sama da 42,200 ga waxanda suka lashe gasar, sannan an fitar da wasu hotunan masu kyawun gaske guda 20. An sanya alqalai na kwamitin qwararrun masana harkar sarrafa hotuna, waxanda suka haxa da mai xaukar hoton Shugaban qasar Najeriya na qashin kasansa da jami’in hulxa da jama’a, waxanda daga bisani suka tantance suka zavo hotunan da suka fi kyawu da qayatarwa, waxanda aka ba su martabar lashe gasar. Jakada W. Stuart Symington ya bayyana waxanda suka samu nasarar lashe gasar xaukar hotunan wurare da abubuwa masu qayatarwa a Najeriya, ta NaijaGEMs, inda a wani faifan bidiyo da ya fito ranar 28 ga Yuni. Jami’in hulxa da ajma’a na ofishin Jakadanci ya miqa shaidun shiga gasar ga fitattun mutanen da suka fafata su 20, sannan an bayar da kyaututtuka ga gwarazan gasar a ranar 6 ga Mayu. Mista Ikechukwu Okeagu ya karvi kyautar martaba ta uku. Mista Matthias Aragbadashi ne ya karvi kyautar martaba ta biyu a gasar. Sai Mista Rimamkongende Shamaki wanda ya lashe babbar kyautar, wato martaba ta xaya. Managarta 50 da suka fafata a gasar, waxanda aka baje hotunan da suka xauka a baje-kolin da aka gudanar cikin kwana bakwai a Abuja, wanda aka fara ranar 6 ga Yuli, inda aka gudanar da bikin bayar da kyaututtuka. Kafafen yaxa labaran Najeriya sun xauki labarin buxe gasar shirin, sannan ya samu halartar iyalai da waxanda suka fafata gasar, da waxanda suka halarci shirin musayar fasaha na Amurka, da Jami’an tuntuva a ofishin Jakadanci, tare da ximbin al’umma. An wallafa wani qaramin littafi xauke da managrtan masu xaukar hoto 50 da suka fafata gasar xaukar hotunan abubuwa da wurare masu qayatarwa a Najeriya, wadda aka yi wa laqabi da ‘NaijaGEMs top 50-photo exhibit’ kuma za a nuna shi a xaukacin biranen Najeriya. A cikin waxannan shafuka za ku karanta labaran wasu daga cikin waxanda suka samu nasarar lashe gasar, sannan za ku ga fitattun managarta 20 da suka fafata a gasar. A xaura xamarar bin kadin al’amura don tantance al’amura masu qayatarwa. MAGAMA | Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman 5