SAQON JAKADA
M
araba da sabuwar fitowar Magama
Wannan haqiqa fitowa ce ta musamman
saboda a cikinta za ku ga bayanin waxanda
suka lashe gasar xaukar hotunan abubuwa
da wurare masu ban ta’ajibi da qayatarwa a
Najeriya, wato gasar da a Ingilishi aka yi wa
laqabin “NaijaGEMs.” Waxannan hotuna sun fito da kyakkyawan
yanayin rayuwar Najeriya, sannan sun yi nuni da qwarewar
qawata hoto na ’yan Najeriya masu sana’ar xaukar hoto, waxanda
suka samar da su. Tabbas na yi matuqar sa’a wajen ganin
kyakkyawan yanayi mai ban sha’awa kaitsaye. A kowane lokaci,
abin da kawai nake nuni da shi a furuci: ina cike mamaki!
W. Stuart Symington
Jakadan Amurka a Najeriya
MAGAMA
Ana wallafa ta ne a bayan kowane wata
uku a sashen Hulxa da Jama’a na Ofishin
Jakadancin Amurka a Najeriya
TAWAGAR EDITOCI
Aruna Amirthanayagam
(Mai Bayar da Shawar kan Hulxa da Jama’a)
Russell Brooks
(Jami’in Hulxa da Jama’a a Legas)
Gleen Guimond
(Jami’in Aikin Jarida)
Olaoluwa Aworinde
(Edita da Daukar Hoto)
Xaukacin sakonni a aike ta
wannan adireshi:
Ga Editan, Mujallar Magama
Sashen Hulxa da Jama’a na Ofishin
Jakadancin Amurka
Plot 1075 Diplomatic Drive,
Central Business Area, Abuja, Nigeria
Tel: (09) 461-4000. Fax: 09-461-4305
OFISHIN LAGOS:
Ofishin Jakadancin Amurka
2, Walter Carrington Crescent, Lagos
Tel.: +234-703-150-4867/2444
E-mail: [email protected]
Website: ng.usembassy.gov
Za ku fara bibiyar duba zavavvun hotunan albarkatun qasa a
Najeriya. Ina mai fatan za ku ji daxin kai-kawon wannan ‘nazari’
sannan ina roqon abu guda bayan haka. Ina son ku haxa qarfi
da waxanda suka jajirce wajen dubawa tare da sauran ’yan
Najeriya wajen alkinta irin waxannan managartan abubuwa da
wurare (da ke cikin muhallinku) da ’yan Najeriya suka gano. A
qarshe ina fatan za ku taya ni yin godiya ga waxanda suka xauko
hotunan, ta wajen ce musu shirin “NaijaGEMs,” ya qayatar!
A wannan fitowar
Bugu na 22 Lamba na 3
Yadda al’amura
suka wakana Shafi na 5
MafI
qayatarwa 10
Shafi na 12
Sarki Kongs
MafI
qayatarwa 20
Shafi na 6
Hoton da
ya lashe
gasa
Shafi na 8
Fatata gasa
Shafi na 16
Alqalai
Shafi na 18
Baje-koli
A biyo mu:
Shafi na 10
Shafi na 2 da 19
MAGAMA | Nuwamba 2018 Fituwa Ta Musamman
3